MAYE HUKUNCIN WACCE TAKE KIRAN MIJINTA BABA KO MIJI YAKIRA MATARSA MAMA KO WASU KALAMAI MASU KAMA DA HAKA?



TAMBAYA❓

MAYE HUKUNCIN WACCE TAKE KIRAN MIJINTA BABA KO MIJI YAKIRA MATARSA MAMA KO WASU KALAMAI MASU KAMA DA HAKA?

*AMSA*👇

Miji yacewa matarsa ke babatace ko ke 'yar'uwatace ko ya mamata zai iya daukar zihari, zai kuma iya zama ba zihari bane, gwargwadon niyyar mutum saboda fadin Annabi sallallahu Alaihi wasallam ( dukkan ayyuka saida niyya kowanne mutum akwai abunda ya niyyata). Bukhari da muslim
Galibi miji yakan fadi wadannan kalmomin ne abisa tausasawa matarsa dakuma girmamawa, baya zama zihari, kuma matarsa bata haramta agareshi ba.
Ibnu qudamah rahimahullah yace:Idan miji yace da matarsa, ke kamar mahaifiyata kike, ko kamar babata kike, kuma azuciyarsa yana nufin zihari, to wannan ziharine, a maganar dukkan malamai, amma idan yana nufin karamcine dakuma girmamawa to ba zihari bane, Almugny (6/8).
hakama dazaice ke babata, ko mamata babata.
An tambayi malaman lajnatul da'ima: wasu mutane suna cewa matayensu " ni Dan'uwankine kema 'yar'uwatace, menene hukunci?
Sai suka amsa: Idan miji yacewa matarsa ni dan'uwankine kema 'yar'uwatace, ko ke babatace ko ke kamar babata kike, ko ke awajena kamar babata kike, ko ke kamar 'yar'uwata kike awajena, idan yana nufin karramawa da kuma girmamawa ko sada zumunci, ko kyakkyawan abu ko kuma bashi dawata niyya matukar babu wasu ababe dazasu nuna zihari yake nufi, to abunda yafada ba zihari bane, kuma babu wani abu akansa.
Idan kuma wadannan kalmomin da ire irensu yana nufin zihari dasune, ko an samu wasu ababe dazasu nuna yana nufin zihari yake nufi kamar yafurtasu cikin fushi da yayi da ita, ko kuma yana mata kashedi da gargadine saiya fadesu, to kalmomin ziharine, taharamta agareshi, wajibine kuma yatuba sannan kaffara tawajaba akansa, shine ya 'yanta baiwa, idan babu sai yayi azumi sittin ajere, idan bazai iyaba sai yaciyar da miskinai guda sittin, fatawa lajnatul da',ima ( 20/274).
Wasu malaman sun karhanta miji yacewa matarsa, ya babata, ko ya 'yar'uwata, saboda hadisin da Abu dauda yaruwaito (2210) Wani mutum yacewa matarsa ya 'yar'uwata, sai Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: 'Yar'uwarkace ita! saiya karhanta masa hakan yahaneshi.
Amma abunda yake dai dai shine babu wani karhanci dan miji yafadawa matarsa wadancan kalmomin dan girmamawa da karramawa haka itama dan tagaya masa, saboda hadisin bai ingantaba, Albani ya raunanashi acikin za'ifu Abu dauda.
An tambayi shaik usaimin rahimahullah cewa: Yahalatta ga miji ya cewa matarsa, ya 'yar'uwata dan so kawai, koya babata ko mamata dan so kawai ?
Sai ya amsa: Na'am yahalatta gareshi yace mata ya 'yar'uwata, ko ya babata ko mamata, dawadanda sukai kama da wannan na kalmomi wadanda suke sa soyayyah da kauna, koda wasu malamai sun karhanta miji yafadawa matarsa irin wadannan kalmomi, saidai babu wani dalili na karhancin, saboda dukkan ayyuka saida niyyah, saboda mutum bai niyyaci cewa 'yar'uwarsace ta haramci ba, ko maharramiyyah ba, kawai yayi nufin yanuna mata kauna da soyayyane, duk wani abu dazai janyo kauna da soyayya tsakanin ma'aurata, daka mace ne ko daka namijine, wannan abune da'akeso kuma ake nema tsakanin ma'aurata.
Dan haka babu laifi cikin wadannan kalmomi dan miji yafadawa matarsa su ko ita tagaya masa su, amma aguji fadarsu lokacin bacin rai ko fushi, anan suna iya zama zihari.

Wallahu A'alamu.

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)