KARIYA DAGA SIHIRI



KARIYA DAGA SIHIRI
***********************
Babbar hanyar kariya daga Sharrin Sihiri da Sharrin muggan Aljannu shine, kiyaye dokokin Allah (swt) da kuma Cin Halat tare da kaucewa hanyar Haram.
Bayan Wayannan Hanyoyin akwai Hanyoyi masu yawa na kariya daga Sihiri wayanda Qur'ani da Hadisai sukazo dasu.
Babu Shakkah Qur'ani Shine babban Kariya Daga Sharrin duk wani Mugun mutum da Aljan.
Hakika kiyaye zikirin safe da yamma da zikirin bayan sallah na farilla da zikirin shiga bacci da na tashi daga bacci da zikirin shiga gida dana fita daga gida da zikirin shiga bayan gida da fita daga ciki da duk wani nau'in zikiri yana daya daga cikin Kariya.
Ana so da Safiya idan mutum ya tashi daga bacci ya karanta Falaqi da Nas a lokacin, In shaa Allahu babu wani abu da Zai sameka a wannan Yinin.
Da kuma Karanta wannan Addu'ar "la'ilaha illallahu wahdahu lasharika lahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa ala kulli shai'in kadir" Sau 100 a kowace safiya da kuma yamma.
Wahid Abdussalam Bali ya kawo hirarsu da wani Aljani a cikin littafinsa, sarimul battar shafi na 136 zuwa 137 Inda Yake Cewa, Wani aljani ne da yaso ya raba wani mutum da matarsa.
Sai malamin ya umarci Aljanin da ya fita daga jikin matar sai aljanin yace zai fita amma da
shardi guda.
Sai malamin ya tambaye shi sahradin sai Aljanin yace zan fita in koma jikinka sai malam
yace wa Aljanin, ba damuwa ka fita daga jikinta ka ka komo jikina in zaka iya.
Nan take sai Aljanin ya fashe da
kuka sai malamin ya tambaye shi mai yasa yake kuka? Sai Aljanin yace, "AI BABU WANI ALJANI DA YA ISA YA SHIGA JIKINKA YAU".
Sai Malamin Ya tambayesa saboda me? sai Aljanin yace, "Domin Ka karanta la'ilahaillallahu wahdahu
lasharika lahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa ala kulli shai'in kadir"
Lalle ne Mu kula da Wannan Addu'ar Sosai da Sosai Domin Ni karan kaina na tabbatar da Hakan.
-Shin kana Samun Kasala Wajen Karanta Wannan Addu'ar? Idan har kana Samun kasala wajen Karantata Ga wani sauqi Zauren-Manazarta ya Samo ma.
Ka Nemi Man Zaitun da Garin haltit da Man Ha/Sauda da Ruwan kahl na tuffa sai ka Hadasu wuri guda Ka karanta Falaqi da Nasi tare da wannan Addu'ar a cikin hadin.
Sai ka rika shafawa duk safiya da Marece In Shaa Allahu Allah zai tsareka daga duk wani Sharrin Mutum ko Aljan kuma Allah zai tsareka daga Sharrin Masihirta.
Muna Rokon Allah ya karemu daga duk wani abinqi.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)