HUKUNCIN WANDA YAKE SHAN NONON MATARSA
*TAMBAYA* ❓
Assalamu alaikum malam macece a duk lokacin da su sadu da mijinta nonon ta kawai yake sha kuma gashi tana da karamar jinjira wai har ya kan shanye ruwan nonon duka yarinyar bata samun nasha idan har tafiya zai yi yakan so ta tatsi nonon ta bashi ya tafi da shi to wai dan Allah ya wannan alamarin ya ke a musulunci meye kuma matsayin wannan dan Allah ina jiran mafita.
*AMSA* 👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Miji ya tsotsi nonon matarsa yayin da suke gabatar da sunnah wannan addini bai haramta ba. Sai dai kuma bai kamata shi mijin nata ya mayar da nonon tamkar abincinsa ba.
Wannan yazo da bakon abu wanda zai iya zama chutuwa agareshi ko ga ita matar tasa ko kuma yarinyar da take shayarwa.
Don haka ya kamata yaji tsoron Allah ya dena ketare iyaka. Mutum ya tsaya inda addininsa ya tsaida shi, kuma ya kyautata Dukkan mu'amalarsa ta auratayya.
Shan nono wanda yaje haramta aure shine wanda aka yishi alokacin da mutum yake yaro karami bai isa yaye ba. Kuma sai ansha kamar sai biyar (cikakkun sha tare da koshi).
Shari'a ta halasta wa mutum ya ji daÉ—i da matarsa gwargwadon yadda ya so, amma ba tare da saduwa ta dubura, da kuma lokacin haila da nifasi, da lokacin harama da aikin Umra da Hajji ba, abin da ba wannan ba ya halasta miji ya ji daÉ—i da shi a jikin matarsa gwargwadon buqata, kamar sumbanta, da kallo da shafa da makamantansu.
Hatta mutum ya sha nonon matarsa duk yana daga cikin jin daÉ—i halastacce, ba a hukunta shi da irin hukuncin shayar da qaramin yaron da bai cika shekaru biyu ba, domin shayar da babba nono ba ya tasiri wurin haramta abin da shayarwa kan haramta, nau'in shayarwar da ke tasiri shi ne shayarwar da aka yi wa yaron da bai cika shekara biyu ba.
An tambayi malaman Lajnatud Dá'ima cewa: Mene ne hukuncin addini game da mutumin da kan ji daɗi da nonon matarsa har ya sha, shin abin da ya yi haramun ne ko halas, shin idan ruwan nonon matar nan ya isa zuwa hanjin mijin nan ta haramta a gare shi sai an raba auren?
Sai suka ba da amsa da cewa:
"Ya halasta ga miji ya sha nonon matarsa, haramci ba ya aukuwa saboda isar ruwan nono zuwa hanjinsa".
Duba Fataáwaál Lajnatid Dá'ima 19/351.
Sannan an tambayi Sheikh Ibn Jibreen game da wannan matsalar sai ya ba da amsa da cewa:
"Shayar da babba ba ya tasiri, domin shayarwar da ke tasiri shi ne wanda ya kasance an yi sau biyar ko fiye a cikin shekaru biyu kafin yaye, amma shayar da babba ba ya tasiri, saboda haka, in da wani zai sha daga nonon matarsa, to shi fa bai zama É—anta ba".
Duba Fataáwá Islamiyya 3/338.
Imamuna MALIK ya ruwaito a cikin MuwaÉ—É—a daga hadisin Abdullahi É—an Umar ya kasance yana cewa: "Babu hukuncin shayarwa sai ga wanda aka shayar yana qarami, kuma ba hukuncin shayarwa ga babba".
Duba MuwaÉ—É—a 2/603 na Imamu Malik.
Bisa dogaro da waÉ—annan dalilai babu laifi don mutum ya sha nonon matarsa, sai dai da za a tsotsa ba tare da shan ruwan ba hakan ya fi, amma shan ba laifi ba ne kamar yadda malamai suka bayyana.
Allah S.W.T ne mafi sani.
_Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana._
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177