MACE CE MAI AURE TAI ZINA DAWANI ALOKACIN SAI CIKI YA SHIGA KUMA TASANI SAITA HAIFE YARON SHIN YARON NA MIJIN AURE NE KONA ZINAR?.



*TAMBAYA*❓

MACE CE MAI AURE TAI ZINA DAWANI ALOKACIN SAI CIKI YA SHIGA KUMA TASANI SAITA HAIFE YARON SHIN YARON NA MIJIN AURE NE KONA ZINAR?.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﻭﻻ ﻋﺪﻭﺍﻥ ﺇﻻ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻈﺎﻟﻤﻴﻦ .

*AMSA*👇

Babu makawa abunda ta aikata na zina tana matar aure yana cikin manyan laifuka, koda zina zunubi ce maigirma ita kadai to girman zunubin nakaruwa idan akace mai aure tayi zina, shiyasa ma hukuncin mazinacin da bai taba aure ba shine bulala 100, wanda kuma yake da aure ko yataba aure shine ajefeshi harsai ya mutu.
Tare da girman laifin data aikata da muninsa a al'ada da kuma hankali, babu wanda zai shiga tsakanin Allah da bawansa Allah yana farin ciki da tuban bawa kuma yana karbar tuban, Allah madaukakin sarki yace:
( ﻗﻞ ﻳﺂ ﻋﺒﺎﺩﻱ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﺳﺮﺍﻓﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ ﻻ ﺗﻘﻨﻄﻮﺍ ﻣﻦ ﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻐﻔﺮ ﺍﻟﺬﻧﻮﺏ ﺟﻤﻴﻌﺎ )
Kagaya musu ya Annabi sallallahu Alaihi wasallam yaku bayina wadanda kuka wuce gona da iri wajan aikata sabo kada ku debe tsammani daka rahmar Allah lallai Allah yana gafarta zunubai gaba dayansu, komai girmansu.
*Ibnu kasir rahimahullah* yace: Wannan aya tana kirane ga dukkan masu sabo harda kafirai su tuba su koma zuwa ga Allah , tana kuma bada labarin Allah yana gafarta zunubai baki daya ga duk wanda ya tuba yadawo daka aikata laifukan, komai irin yawansu da girmansu koda sunkai yawan kumfar kogi, matukar anyi tuba nagaskiya Allah yana gafarta su.
Amma nasabar ɗan za'a jingina shi ga mijinki na aure ne, matukar yasadu dake , saboda faɗin Annabi sallallahu Alaihi wasallam dayace: ,( Ɗa na me aurene,) ma'ana ɗan na mijin dakike aure dashine koda ba'a saduwa dashi cikin ɗan ya shiga ba, indai kin kwanta da mijin bayan zinar ɗan nasane.
*An tambayi shaik bin baaz dangane da matar datake da aure kuma tanada 'ya'ya uku, ɗa nahudun saita samu cikinsa ta hanyar zina, shin ya halatta ta zubda cikin ɗan? ko zata kyaleshi idan ta kyale cikin shin zata baiwa mijinta labari ko bazata bashi ba? sannan menene yake wajibi akan mijin a wannan halin?.*
Sai ya amsa dacewa: Bai halatta agareta ta zubda wannan cikin ba, abunda yake wajibi akanta shine tuba zuwa ga Allah madaukakin sarki, da kuma kin bayyana al'amarin, ɗan data haifa kuma za'a jinginawa mijinta ma'ana ɗansane, saboda fadi6n Annabi sallahu Alaihi wasallam ( Ɗa na mai aure ne mazinaci kuma uquba ce kawai tasa) Ma'ana wanda yai zina baida hakkin ajingina ɗan gareshi, shi kawai uqubar zinarce akansa.
*Fatawa bin bãaz (21/205).*
Da wannan majalisar fatawa ta kasar saudiyyah tai fatawa, Allah yagyara halayen mu gaba ɗaya.

Wallahu A'alamu.

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ ﻧﺸﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ ﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﻧﺘﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ .

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)