JINI YA BARKE MIN, SABODA AN YI MIN WANKIN CIKI?



JINI YA BARKE MIN, SABODA AN YI MIN WANKIN CIKI?

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum Dan Allah inada tambaya macen da tayi bari aka mata wankin ciki bayan nan sai jini yake zuwa mata yadai baiyana jinin ciwo ne Shin zata dunga wanka ne lokacin da zatayi kowace sallah? Ko kuwa tsarki kawai zatayi lokacin sallah?   

*AMSA*👇

To dan'uwa Za ta yi tsarki kuma ta yi alwala ya yın kowacce sallah, saboda hukuncinsu É—aya da mai istihâlâ, kamar yadda Annabi saw ya umarci Fadimatu 'yar Abi-Hubaish a hadisin Ibnu Hibban mai lamba ta: 1354, da yın alwala yayin kowacce sallah, lokacin da ya tabbatar tana yın jinin cuta.

Don neman karin bayani duba: Risala Fi Dima'u Addabi'iyya: 45

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaÉ—a wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)