Sahabban Annabi (ﷺ): Allah Yana Kiran Su Da Sunan Imani



Ramadaniyyat 1442 H [26]

Dr Muhd Sani Umar (Hafizahullah)

Sahabban Annabi (ﷺ): Allah Yana Kiran Su Da Sunan Imani
______________________________

1. Bayan Allah (SWT) ya bayar da labarin abin da ya faru tsakanin Ausu da Khazraju, da babbar ni'imar da ya yi musu ta samar musu hadin kai a tsakaninsu, bayan da sun kasance ba sa ga miciji a junansu. Sai kuma ya ce: (Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi takawa ga Allah hakikanin takawa, kuma lalle kada ku mutu face kuna Musulmi) [Ali Imran: 102]
2. Wannan kira ne da Allah (SWT) yake yi wa sahabban Annabi (ﷺ) saboda su ne farkon wannan al’umma, duk wadanda za su zo a bayansu, idan sun yi imani da Allah da Manzonsa, to su ma sun shiga karkashin wannan kiran. 
3. A wannan ayar Allah (SWT) ya yi kira ga muminai duka da su kiyaye dokinsa, su yi abin da ya umarce su, su guji abin da ya hana, su kuma rungumi Musulunci har zuwa mutuwarsu, saboda dan’adam bai san sanda zai mutu ba, kamar yadda Allah (swt) ya ce: (Ba kuma wani rai da yake sane da kasar da zai mutu. Lalle Allah Shi ne Masani, Mai cikakken ilimi) [Lukman: 34]. 
4. Sayyadina Abubakar (RA) kuma yana cewa:
"Kowane mutum yakan wayi gari da safe cikin iyalansa,
alhali mutuwa kuma tafi igiyar takalminsa kusanci da shi".
Watau a kowane lokaci mutum zai iya mutuwa. To idan ya zamanto haka ne, to wajibi ne mutum ya kasance a cikin shiri koyaushe. Saboda haka da Allah ya ce: (kuma lalle kada ku mutu face kuna Musulmi) [Ali Imrana, aya ta 102].
Watau kowane lokaci ku kusance kuna cikin addini, domin a kowane lokaci za ku iya mutuwa, ka da mutuwar ta riske ku ba kuna Musulmi ba, don haka ku dawwama da riko da Musuluncin. 
5. Sai Allah ya ce:
 (Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada kuma ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya hada tsakanin zukatanku, sai kuka zamo 'yan’uwan juna a sakamakon ni'imarsa, a da kuma kun kasance a kan gabar ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa don ko kwa shiriya.) [Ali Imran: 103] 
6. A nan ana kiran al’umma ne gaba dayansu, amma da fari dai ana magana ne da kabilar Ausu da Khazraju, wadanda suka riki Musulunci bayan sun watsar da gabar dake tsakaninsu, da yake-yakensu na jahiliyya. To shi ne Allah yake kara fada musu cewa, su yi riko da igiyar Allah, watau imaninsu da Allah da addinin Musulunci da suka karba. Watau ya zamanto abu guda ne zai hada kansu shi ne Musulunci. Ya nuna musu cewa, su zubar da maganar kabilanci da bangaranci da kowane abu, su dawo su rike Musulunci, su dunkule su zama abu daya.
7. Don haka Allah ya tabbatar musu cewa, matukar sun rike igiyar Musulunci gaba dayansu, to har abad za su ci gaba da zama tsintsiya madaurinki daya. 
8. Wannan ya sa Annabi (ﷺ) ya gargade su da cewa: “Kada ku koma a bayana kamar kafirai, sashin ku yana yakar sa shi.” A nan ba yana nuna cewa, idan sun yi fada a junansu sun kafirta ba, a’a yana nufin za su koma kamar kafirai wadanda sashinsu yake yakar sashi.
9. Sai Allah ya ce: (kada kuma ku rarraba.) 
Wannan yake kara nuna cewa da Allah ya ce “wa atasimu” yana nufin a hadu duka, ba wai kowa ya rike shi kadai ba, saboda idan an ce kowa ya rike shi kadai, to “wa la tafarraku” ba ta da ma’ana. Amma idan ana nufin dukkan ku hadu ku rike igiya daya, to shi ne kun zama abu daya, yayin da kuma ku ka rarrabu, to babu shakka ko dai ku duka kun saki igiyar ko kuma wasu sun saki sun koma gefe guda.
10. Saboda haka Allah yana nuna musu cewa, Musulunci ne kadai abin da zai hada kansu, duk wani abin da za su rike da sunan za su samu hadin kai, ba zai amfane su ba.
11. Shi ya sa a koyaushe idan ana so a hada kan Musulmi, to a dawo kan Musuluncin, shi ne abin da zai hada kan musulmi. Amma duk wani abu da za a yi a ce za a hada kai, to wannna magana ce ta fatar baki kawai, kamar yadda Allah ya siffanta munafukai da cewa: (Za ka tsammaci kansu a hade yake, alhali zukatansu a rarrabe suke. Wannan kuwa saboda cewar su mutane ne da ba sa hankalta.) [Hashr: 14]

https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)