YA HALATTA MATA TA YI WA MIJINTA ADDU'A ALLAH YA WARGAZA AUREN DA YAKE NEMA



*_TAMBAYA TA 2124_*👇

Assalamu alaikum. Malam ya dawainiya Allah ya taimaka. Tambayata Dan Allah ita ce shin ya halatta mata ta yi wa mijinta addua akan kar Allah ya wargaza naiman auren da ya k yi saboda wasu dalilai kamar haka: 
Uwar yarinyar kowa ya santa da bin bokaye wanda shima ya tabbatar min da hakan amma sai ya ce ba lalle yarinyar ta yi halin uwarta ba. 
 Ita kanta yarinyar ba wani son sa ta k yi ba abin hannunsa ta k so domin yau ta ce ta fasa aurensa ba dalili idan an kwana biyu kuma sai ta naime shi su shirya Wanda shima an tabbatar da ba wani sonshi ta k ba shi kansa ya aha min complain. Sannan kuma malam kullum zai ce uzurin rabuwa da ita ya k naima amma idan ta ce ta fassa aurensa yakan shiga damuwar da mu ma abin yana shafarmu. kuma maganar gaskiya mutum ne shi mai rauni a wurin ibada. idan ka ce yayi sallah ya fada ma ubangiji ba zai yuwu ba sai dai ya yi ta juyi akan gado. Shi ya halatta malam dan Allah na dinga Addua a cikin sujjada akan Allah ya fitar masa ita a ransa? Nagode Allah ya saka da aljannatul firdausi

*_AMSA_*👇

_Wa'alaikum salam warahmatullah_

_Idan har abubuwan da kika bayyana duk gaskiya ne, tho ya halatta kiyi masa wannan addu'ar sannan ki kara da Ubangiji ya canza masa da wacce take mafi alkhairi, bayan haka sai ki jajirce wurin nema masa wacce ta dace kuma kiyi kokari wurin ganin hakan ya tabbata ta duk hanyar da zaki iya. Amma kisani ba dai-dai bane ki hanashi aikata abinda Ubangiji ya halatta masa ba, domin bakisan dalilin da yasa yace zai kara auren ba, kada hanashin ya sanya ki zama silar sanyashi cikin halaka. Abu na karshe shine duk wanda ya tashi neman aure, tho ba iya yarinyar da za a aure ake bincika kadai ba, hatta iyayen yarinyar, da zarar bincike ya tabbatar cewa yarinyar tanada kirki amma mahaifiyarta batada kirki, tho wajibine ka rabu da ita, domin mahaifiyarta zatayi tasiri akanta yayin da kika aureshi, wanda daga karshe ma ka iya sakinta, saboda haka duk nagartan mace indai mahaifiyarta ba nagarta bace, ba mutuniyar kirki bace, tho ina me baka shawara akan ka canza wata, domin munsan abubuwan da bakusaniba gameda matsalar. Allah Ubangiji yayi mana jagora._

_WALLAHU A'ALAM_

 Daga👇
*ZAUREN SUNNAH GROUP*

*مجلس السنة*

📓📔
Whatsapp
+2349032091131
+2348067812397
+2348167807912
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
https://t.me/joinchat/Q6e80xgzT5D_uuqsGlk3eA

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليه.
Post a Comment (0)