YADDA AKEYIN SUJJADAR QABLI DA SUJJADAR BA’ADI*
*TAMBAYA*❓
Ina san Karin bayani akan sijjada ba adi da kabali
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
1. Sujjada Qabli : ana yinta ne kafin sallama. Bayan mutum yayi tahiya, kafin yayi sallama, sai ya sake yin wasu sujjudu guda biyu, sannan ya sake yin wata tahiyar, Sannan yayi sallama. Wannan ita ce Sujjadar Qabaliy, Dalilan da suke sawa ayi ta: Idan mutum yayi ragi a cikin Sallarsa, Ko kuma ya tauye wasu sunnoni Qarfafa guda biyu ko sama da haka. (a takaice kenan).
2. SUJJADA BA’ADI : ana yinta ne duk yayin da aka Qara wani abu acikin Sallah. Kokuma yayin da mutum ya mance da wata farillah, ko kuma rukuni daga cikin sallar sa. Bayan ya kawo wannan farillar da ya mance, to sai yayi sujjadar Ba’adi.
*YADDA AKE YINTA :*
Ana yinta ne bayan anyi tahiya anyi sallama, sai a sake yin wasu sujjudu guda biyu, sannan ayi tahiya ayi sallama.
ﺑَـﺎﺏٌ ﻓِﻲ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩِ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ
ﻭَﺃَﻣَّﺎ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﻘَﺒْﻠِﻲُّ ﻓَﺴَﺒْﻌَﺔٌ :
ﻓَﻤَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺗَﻴْﻦِ ﻓَﺄَﻛْﺜَﺮَ ﻏَﻴْﺮَ ﺗَﻜْﺒِﻴﺮَﺓِ ﺍْﻹِﺣْﺮَﺍﻡِ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺳَﻤِﻊَ ﺍﻟﻠﻪُ ﻟِﻤَﻦْ ﺣَﻤِﺪَﻩُ ﻣَﺮَّﺗَﻴْﻦِ ﻓَﺄَﻛْﺜَﺮَ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺍﻟْﺠَﻠْﺴَﺔَ ﺍﻟْﻮُﺳْﻄَﻰ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﺴِﻲَ ﺍَﻟﺘَّﺸَﻬُّﺪَ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﻧَﻘَﺺَ ﻭَﺯَﺍﺩَ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺃَﺳَﺮَّ ﻓِﻴﻤَﺎ ﻳُﺠْﻬَﺮُ ﻓِﻴﻪِ ﺳَﺠَﺪَ ﻗَﺒْﻞَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ .
ﺍِﻧْﺘَﻬَﻰ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﻘَﺒْﻠِﻲُّ .
*BABIN SUJJADA KAFIN SALLAMA*
Amma Sujjadar Kabli guda bakwai ce: –
1_Wanda ya manta kabbara biyu ko fiye banda kabbarar harama sai ya yi sujjada kabli.
2_Wanda ya manta (faɗin) Sami’allahu liman hamidahu, sau biyu ko fiye ya yi sujjada kabli.
3_Wanda ya manta zaman (tahiya) tsakiya ya yi sujjada kabli.
4_ Wanda ya manta karatun tahiya ya yi sujjada kabli.
5_Wanda ya rage ya qara ya yi sujjada kabli.
6_Wanda ya asirce (karatu) a inda ake bayyana shi ya yi sujjada kabli.
sujjada kabli sun tuke
ﺑَـﺎﺏٌ ﻓِﻲ ﺍ ﻟﺴُّﺠُﻮﺩِ ﺍﻟْﺒَﻌْﺪِﻱِّ :
ﻭَﺃَﻣَّﺎ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﺒَﻌْﺪِﻱُّ ﻓَﺴَﺒْﻌَﺔٌ :
ﻭَﻣَﻦْ ﺗَﻜَﻠَّﻢَ ﺳَﺎﻫِﻴًﺎ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺳَﻠَّﻢَ ﻣِﻦْ ﺭَﻛْﻌَﺘَﻴْﻦِ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺯَﺍﺩَ ﺭَﻛْﻌَﺔً ﺃَﻭْ ﺭَﻛْﻌَﺘَﻴْﻦِ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺍِﺳْﺘَﻨْﻜَﺤَﻪُ ﺍﻟﺸَّﻚُّ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺟَﻬَﺮَ ﻓِﻴﻤَﺎ ﻳُﺴَﺮُّ ﻓِﻴﻪِ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ، ﻭَﻣَﻦْ ﺟَﻠَﺲَ ﻓِﻲ ﺍﻟﺮَّﻛْﻌَﺔِ ﺍْﻷُﻭﻟَﻰ ﺳَﺠَﺪَ ﺑَﻌْﺪَ ﺍﻟﺴَّﻼَﻡِ .
ﺍِﻧْﺘَﻬَﻰ ﺍﻟﺴُّﺠُﻮﺩُ ﺍﻟْﺒَﻌْﺪِﻱُّ .
*BABIN SUJJADA BAYAN SALLAMA*
Amma sujjada bayan sallama guda bakwai ce: –
1_Wanda ya yi zance da mantuwa ya yi sujjada ba’adi.
2_Wanda ya yi sallama a raka’a ta biyu yayi sujjada ba’adi.
3_Wanda ya kara raka’a ɗaya ko biyu ya yi sujjada ba’adi.
4_Wanda kokwanto ya aure shi ya yi sujjada