Yadda Ake Zakkar Gidan Haya Da Motar Haya



Yadda Ake Zakkar Gidan Haya Da Motar Haya
:
TAMBAYA❓
:
Assalamu alaikum Malam Shin ko akwai zakka akan Gona, Fili ,Gidan haya da Motar Haya?
:
AMSA👇
:
Waalaikumussalam, To dan’uwa duk gonar da aka rika don ayi amfani da ita, to babu zakka a cikinta, haka nan fili, amma idan kasuwanci ake yi da su, kamar a siya a sayar to za’a fitar musu da zakka, idan sun cika nisabi kuma shekara ta zagayo musu, ko kuma ya zama sun cika sharudan zakka idan ya haÉ—a su da abin da ke hannunsa.

Haka nan babu zakka a cikin gidan haya saidai idan aka tara kuÉ—in kuma shekara ta zagayo akan su, sun cika nisabi, to anan ne za’a fitar musu da zakka, ko kuma ya zama sun cika sharudan zakka idan ya haÉ—a su da abin da ke hannunsa.

Allah ne mafi sani.

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM
Post a Comment (0)