BAYANI AKAN CUTAR TRICHOMONIASIS


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Bayani Aka Wannan Kalan Ciwon Sanyi Da Ake Kira Da TRICHOMONIASIS_*

Itace wacce ake yadawa ta hanyar jima'i ga maza (STD)musamman idan ana neman matan banza shine take yaudwa sosai adunia kamar (HIV).
Ana kiran 'yar kankanuwar halittar *Parasitic Organism* itace ke sanya Trichomonas vaginalis.

Maza ba akasafai suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman magani suke gano suna da cutar. Idan anyi sa'a alamomin ciwon sun bayyana ga maza, kamar haka:

*_Alamomin Wannan Ciwon Sanyi Ga Maza_*
* Zubar farin-ruwa kadan,
* Zafi kadan bayan fitsari,
* Zafi kadan bayan fitar maniyyi.

*_Alamomin Wannan Ciwon Sanyi Ga Mata_*
1.zubar ruwa mai launin tsanwa.
2.zubar ruwa mai launin dorawa.
3.zubar ruwa mai kumfa da wari.
4.zafi wajen yin fitsari,
5.rashin jin dadi wajen jima'i.
Sannan kuma alamomin cutar ga mata suna iya kama da ciwon sanyi na 1 da na 2 wanda nayi bayani a sama, Wannan cuta tana da hadari ga mace mai ciki ga abunda ke cikinta, musamman idan ba'a nemi magani ba.


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*


*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a shiga ta wannan link din* 👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/GqtP5PUubzCHPlL92GDFT1
Post a Comment (0)