ANNABI DA SAHABBANSA // 081



ANNABI DA SAHABBANSA // 081
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
AN SA RANAR YAQI NA GABA
Galibin abin da mutane suka sani shi ne an yi yaqe-yaqe a zamanin Annabi SAW, sannan ga shi ana cewa ba da takobi aka yada muslunci ba ya abin yake ne? Da za a sa idon natsuwa za a ga cewa a Badar dai Quraishawa ne suka shiryo wa yaqin daga Makka, Annabi SAW da sahabbansa suka fito don maido da haqqinsu daga fataken Sham, sai suka yi gamo da yaqin da ba su shirya masa ba, shi ya sa wadan da suke Madina ba su ma san me ya faru ba, a Uhud ma Quraishawan ne dai suka zo gamawa da musulmai Allah SW ya taimake su ya ba su kariya.
.
Gama wannan yaqi Abu-Sufyan ya ce "Mu hadu badi a Badar" Annabi SAW ya ce a gaya masa cewa "Mun ji mun amsa mu hadu a can badi din" daga nan Abu-Sufyan ya ja rundunarsa suka kama hanya (Ibn Hisham 2/94), Annabi SAW ya sanya Aliy RA ya bi bayansu ya ga abin da suke ciki, in suka bar dawaki suka hau raquma to Makka za su koma, in kuwa suka yi zamansu a kan dawaki suna kada raquman to Madina za su kwano.
.
Da Aliy ya bi su sai ya ga sun hau raquman ne sun fuskanci Makka, don haka musulmai suka fara duba gawawwakinsu don sanin masu shahada da kuma birne su, Zaid bn Thaabit ya ce "Annabi SAW ya tura ni na binciko Sa'ad bnr Rabee' ya ce in ka gan shi ka gaida min da shi ka tambaya min jikinsa" Zaid ya ce na fara bincika gawawwaki a qarshe dai na samo shi.
.
Ya ce "Na same shi da rauni har guda 70, wasu sara ne da takobi sai suka da masu, wasu kuma harbi ne da kibiya, na ce masa " Sa'ad Annabi SAW na gaishe ka, ya ce ya jikin?" Ya ce "Ina amsa gaisuwar Manzon Allah SAW ka ce masa ina jin qamshin aljanna, ka kuma gaya wa mutanena Ansarawa: Ba ku da wani hanzari in aka kai ga Annabi SAW alhali idanunku suna iya qiftawa, daga nan Allah ya yi masa cikawa (Zadul Mi'ad 2/96).
.
A cikin masu raunukan ne dai aka samo Usairim wato Amr bn Thaabit, yana da dan sauran numfashi, da sun yi ta yi masa tayin muslunci yana bijirewa, don haka suka ce "Wai me ya kawo wannan ne? Mun fa bar shi yana qin muslunci" sai suka tambaye shi "Ka zo don kishin jama'arka ne ko don kwadayin muslunci?" Ya ce "Kwadayin muslunci ya kawo ni, tuni na yi imani da Allah da manzonsa, na kuma yi yaqi tare da Annabi SAW har wannan ya same ni" bai jima ba ya rasu, da aka gaya wa Annabi SAW sai ya ce yana cikin 'yan aljanna, mun kawo maganarsa a baya, Abuhuraira ya ce bai taba yin salla ba.
.
Haka kuma aka sami Qazmaan cikin masu jinjiki, ba shakka ya yi duk jarumtar da ake buqata, shi kadai ya kashe mushrikai wajen 7-8, amma raunin da aka yi masa ya riga ya illata shi, aka dauke shi zuwa gidan Banu Zafar, musulmai suka kwadaitar da shi muslunci da shahada, amma ya ce shi don qabilarsa kadai ya yi yaqin, in ba don haka ba da bai yi ba, a qarshe dai haka ya mutu, da aka gaya wa Annabi SAW ya ce dan wuta ne.
.
Wannan shi ne babban dalilin da ya sa qasa mai tsarki wato Saudiyya ta qi shiga yaqin Palestine, don su sun ce matsalar qasarsu ce a matsayinsu na Larabawa, in da za mu lura da Yemen, Bahrain da Syria ba haka abin yake ba, da a ce za su mai da abin a matsayin haqqi na muslunci da wannan ya zama alhaki a wuyar duk wani musulmi, nan ne za ka ga shedancin qasar Iran, Palasdinawa sunni ne, kuma Larabawa ne, su Shi'a da sunni ne abokan gabansu na farko ya za a yi su ce za su taimaki Palestine? Sai sanyawa suke yi ana kashe su ba su taba shugowa an yi da su ba.
.
An kuma sami Bayahude daya da ya shugo cikin musulmai aka yi yaqin da shi, har aka kai shi lahira, daga cikin Banu Tha'alaba yake, ya sami mutanensa ya ce musu "Ku Yahudawa ku sani taimakon Muhammad abu ne a kanku da ya zama wajibi, suka ce "To dai yau asabar ce" ya ce "Ba wata Asabar" ya dauki takobinsa da kayan shirinsa ya kama hanya, ya ce "In aka kashe ni to a ba Muhammad dukiyata ya yi abin da yake so da ita" ya ci gaba ya yi ta yaqin har aka kashe shi, sai Annabi SAW ya ce "Duk a Yahudawa Mukhaireeq ne na qwarai" (Ibn Hisham 2/88-89)

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)