ANNABI DA SAHABBANSA // 080



ANNABI DA SAHABBANSA // 080
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
YAQI YA QARE
Yanzu ba wanda zai iya fassara wannan yaqin a daidai wannan lokacin kuma ya ce Annabi SAW da sahabbansa RA ba su yi nasara ba, duk kuwa da baqar wahalar da aka sha, domin ba burin mushrikai da ya cika ko qwara daya, (1) Duk yawansu na banza ne ko mutum nawa suka kashe ba su iya zuwa ko ganuwar Madina ba bare su shiga bare kuma su ce sun bi musulmai har gidansu sun ci su da yaqi, (2) Duk kisar da za su ce sun yi ba su iya kama ko fursunoni ba bare su ce a yi musaya da na Badar.
.
(3) Koda a ce sahabbai sun mutu, ba manyan da suke son kashewa ba ne, tabbas Hamza RA ya yi shahada, kuma babba ne, amma in aka ce Abubakar RA da Umar RA da uwa-uba Annabi SAW yana da rai sai mu ga ba wata murnan da za su yi don sun kashe shi, tunda tun asali ma ba shi a jerin sunayen wadan da ake da burin kai su lahiran, (4) Ko sun yi kisa babu wata ganima, tana daya daga cikin alamun dake nuna samun nasara a kan abokan gaba, idan kuwa aka ce nasu aka samu to ba ko shakka lamarin ya sauya zane.
.
(5) Yakamata a ce sun fatattaki musulmai don su ne suka ci nasarar yaqi, in har aka ce su ne suka runtuma a guje suka bar ladarsu to ko shakka babu su aka ci nasararsu, (6) Zai yi kyau duk mai karatu ya sake tuna cewa musulmi fa ya fito ne don ya kare kansa daga mahara, in har ya iya hana shiga qasarsa, jagororinsa suka dawo gida lafiya, ya kare rayukan tsahhi, mata da yara qanana to shi ya ci ribar yaqi.
.
A qarshe in da sahabbai RA sun diba a guje sun bar Annabi SAW shi kadai a fagen fama sai Aliy RA a gaban mutum 3,000 da wallahi ba wannan maganar muke yi ba, ko a Hollywood mutum 2 ba sa yaqi da 3,000 bare wannan da yake jarabawa ne daga mahalicci, dubi yadda yaqin ya kasance, ka yi wa tatsuniyar 'yan Shi'a kunnen uwar shegu, sahabbai RA ba su taba saba wa Allah SW da manzonsa don son zuciya ba, wannan ne ma ya sa Allah SW ya sanya nasara a hannunsu, in ka karanta qissar Ka'ab bn Malik a Bukhari ko Riyadus Salihin.
.
To don Allah ka koma tarihin muslunci ka duba ko waye wannan sahabin a yaqin Uhud shi da masoyinsa Talha, ka bi yaqin da irin abin da ya faru don kasan jarumtarsa ko rauninsa, wallahi nan ne zaka san dalilin da yasa Rumawa suka yi zawarcinsa har suka buqaci ya rabu da Annabi SAW ya je wurinsu, in don 'yan Shi'a ne ka tambaye su wadan da suka amince da su a sahabbai, in sun gaya maka ka ce "To wadannan ne suka yaqi Quraishawa 3,000 ko akwai wasu? Tunda sun ce sahabbai sun gudu sun bar Annabi SAW"
.
YAQI YA KOMA SURKULLE
Bayan yanke-yanken da wasu suka yi wa gawawwakin musulmai sai gaggan Quraishawan suka koma kan dutse, sauran mushrikan suna kan hanyar komawa gida, Abu-Sufyan yana kan dutse ya daga murya "Wai Muhammad na raye a cikinku?" Ba wanda ya amsa masa, dan Abu-Quhaafa (Abubakar RA) na nan?" Shi ma suka yi banza da shi.
.
Ya sake cewa "Shin Umar bnl Kattab yana cikinku?" Ba wanda ya tanka masa, don Annabi SAW ya riga ya ce musu su fita harkarsa daga nan bai sake tambayar kowa ba sai wadannan ukun, ashe ko a tsakankanunsu suna sane cewa wadannan su ne jagororin musluncin, wadan da sam addini ba zai taba tsayuwa ba sai da su, to in kafuri ma ya san haka ya za a yi wannan ya buya wa musulmi in dai har musulmin ne na qwarai ba musulmiya ba?
.
Umar RA bai iya danne zuciyarsa ba sai da ya maida musu da martani "Kai abokin gaban Allah! Duk wadan da ka lissafo suna da ransu, sai dai ka mutu Allah bai kashe su ba" bai ba da wannan amsar ba sai ya ce "An yayyanke gawawwakinku koda yake ban yi umurni da haka ba amma ban damu ba" sai ya ci gaba da cewa "Kai sai Hubal" Annabi SAW ya ce "Ku ba shi amsa mana!" Suka ce me za mu ce masa?" Ya ce "Ku ce Allah ne mafi girma da daukaka"
.
Ya ce "Weeee! Muna da Uzza ku ba ku da ita!" Annabi SAW ya ce "Ku amsa masa, ku ce Allah ne majibancinmu ku kuma ba ku da shi" ya ce "Oho dai mun rama abin da aka yi mana a Badar, yau a naka gobe a na wani" Umar RA ya ce "I, mamatanmu na aljanna ku kuwa naku na wuta" ya ce "Umar ya fito nan" Annabi SAW ya ce "Je ka ji me zai ce" da ya fito ya ce "Don Allah mun kuwa kashe Muhammad?" Ya ce "Ina! Wallahi yana jin abin da kake cewa" ya ce "Na fi gasgata ka sama da Ibn Abi Qam'a" a qarshe haka yaqin ya koma.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)