CIKA ALWALA DA KUSHU'I A CIKIN SALLAH SUNA DAGA SABUBBA SHIGA ALJANNAH! (02)
•┈┈┈••✦💦✦••┈┈┈•
Daga Humraan Ƴantaccen bawan Usman bn Affan cewa shi yaga Usman bn Affan yasa an kawo masa abin alwala, sai ya zuba ruwa akan hannayen sa guda biyu daga kwanan alwalan sa, se ya wanke hannayen sa sau uku, sannan ya shigar da hannunsa na dama a cikin abin alwalan ya kuskure baki ya shaƙa ruwa kuma ya face, sai kuma ya wanke fuskansa sau uku da hannayen sa zuwa gwiwar hannu sau uku sannan se ya shafi kansa, sannan sai ya wanke kowace ƙafa sau uku sannan sai yace; Naga Annabi yana yin alwala kwatanmwacin wannan alwala tawa, sai (Annabi) yace: "Duk wanda ya yi alwala kwatanmwacin wannan alwala tawa sannan ya yi sallah raka'a biyu, bai tattauna wasu abubuwa ba (a ransa) Allah zai gafarta masa dukkan abinda ya gabata na zunuban sa.
-BUKHARI&MUSLIM
Dariqus-Silihin 15pg
Note:
• Cikin wannan alwalan ba'a ambaci shafar kunne ba, Malamai suka ce shafar kunne tana cikin shafar kai (ana haÉ—e su) shi yasa Humraan bai ambaci kunne ba.
• Duk wanda ya yi alwala da irin wannan siga sannan ya yi sallah raka'a biyu ba tare da tunanin duniya ba za'a gafarta masa zunubansa baki É—aya.
• Malamai suka ce, barin tunanin, ai idan tunanin yazo masa cikin sallan se ya danne ya fuskanci sallan sa.
#Zaurenfisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah