HUKUNCIN SHAN TABAR SHISHA

HUKUNCIN SHAN TABAR SHISHA
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum malam dan Allah minene hukuncin shan shisha a musulunci? Dan yanzu naga maza da mata yan mata da samari ta zamo musu sana'a.
(Daga K. Lawal Magaji).
:
*AMSA*👇
:
W/SALAM WA RAHMATULLAH.
Hakika dukkan abinda 'Dan Adam yake Ci ko sha, sun kasu ne zuwa gida biyu.
1. Akwai Tsarkaka Masu Daɗi.
2. Akwai kuma Marassa daɗi, Ko masu Najasa.
Su Tsarkaka masu daɗi sune waɗanda idan Ɗan Adam yayi amfani dasu zasu amfani jikinsa.
Su kuma Marassa tsarki sune irin su Giya, taba, Wiwi, Shisha da Sholisho da duk sauran kayan Maye. Saboda idan kayi amfani dasu ba zasu amfanarka da komai ba. Sai dai ma su cutar da lafiyarka, kuma su cutar da Hankalinka..
Kasancewar tabar Shisha batta amfanar da Ɗan Adam sai dai ma ta cutar dashi, Kuma gashi ana sayenta ne da kudade masu tsada, shi yasa sayenta ya zama Almubazzaranci.
Ubangiji (SWT) yana cewa:
"KAR KUYI ALMUBAZZARANCI. HAKIKA SU MASU ALMUBAZZARANCI SUN KASANCE 'YAN UWAN SHAITANU NE. SHI KUMA SHAITAN YA ZAMANTO YA KAFIRCE MA UBANGIJINSA NE"
Hakika duk musulmi mai hankali ba zai so ya aikata abinda zai mayar dashi ya zama 'Dan uwan Shaitan ba.
Hakanan zukar tabar Wiwi ko Sigari ko Shisha, yana haddasa ma mutum cutar Daji acikin Hunhunsa. wato LUNG CANCER. Wanda yakan zama sanadiyyar mutuwar matasa da dama.
Allah (SWT) YACE : "KAR KU JEFA HANNAYENKU ZUWA GA HALLAKA".
Bai halatta mutum Mai hankali kuma mai Imani ya rika shan irin waɗannan abubuwan ba.

WALLAHU A'ALAM.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ


Post a Comment (0)