YAFIYA



YAFIYA.
-
"Yafiya wata halitta ce wacce Allah yake kimsata a cikin zuƙatan waɗanda yaga dama, wasu mutanen basa yin yafiya a cikin lamuransu kuma basu da haƙuri idan aka taɓa sha'aninsu"
-
"Kayi yafiya kuma ka kawar da kai, wannan shi ne halin magabata na ƙwarai, kada ka damu da cewa sai ka ɗauki fansa a kan wanda ya munana maka, idan wani ya yi maka kuskure kuma ya nemi yafiyarka, to ka yafe masa, da sannu kaima Allah zai yafe maka, domin lallai haƙiƙa tabbas Allah yana so kuma yana tare da masu haƙuri waɗanda suke yin haƙuri wajen ɗa'a ga Allah, kuma suke yin haƙuri ga ƴan uwansu, lallai idan ka yafe tabbas kaima Allah zai yafe maka"
-
"Haƙuri baya taɓa faɗuwa ƙasa, haka nan yafiya alkhairi ce ga al'umma. Duk wanda ya siffantu dasu, to haƙiƙa Allah zai kasance a cikin lamuransa ya dinga tausaya masa, ya Allah ka tausaya mana"
-
Telegram channel
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
Facebook group
https://www.facebook.com/groups/4329860357034439/?ref=share
Post a Comment (0)