AMFANIN GARIN KIMBA GUDA 20

AMFANIN GARIN KIMBA GUDA 20.

 Share Dan Allah




Yauma kamar yanda muka saba mun sake dubane zuwa ga alfanon 'KIMBA' wacce muka tashi muka tarar ana nomawa kuma ana amfani da ita wajen gyaran kayan abinci a gida musamman a yankunnan kasashen Hausawa.Da fatar zamu amfana kuma za muyi shere zuwa ga 'yan uwa da abokai da zasu zamo mabukata ganin ba kowa yasan da faidar wannan kimbar ba.Da dama sun dauketa kayan gyaran abinci ne kawai dan yayi armashi ko dandano ka qamshi wanda amfanin KIMBA ya zarce tinanin mai karatu.

KIMBA tana qumshe da Sinadirrai masu karfin yaqi da qwayoyin cutuka daban daban,kuma suke da muhimmanci ga 
lafiyar jikin dan Adam.kamar su copper, zinc,protein,camphene, limonene,folic acid,flavonoid,vitamin A,B1,B2,C and E.
da makamantansu.

Samuwar wadannan Sinadirran dama wasu magunna a cikin KIMBA yasa ta zamo magani ga cutukka kamar haka :

1. Malaria : A tafasa KIMBA ita kadai sai a tace ruwan a sha rabin karamin Kofi na gilashi,za a sha idan an ci abinci sai a nemi ruwan dumi a yi wanka,za ayi haka safe da yamma.

2. Ciwon ga6o6in jiki A tafasa KIMBA a tarfa Zuma cokali biyu manya a sha.

3. Sanyin kirji,tarin majina,atishewa,kakin majina akai akai na majinar iska ko tari ana ganin jini.

4.Tarin asma,tarin gaida,tarin lala,tarin covid,tarin tibi,tarin nimoniya,tarin bronchitis, tarin shan taba sigari,tarin hayaqi ko shaqar qura ga masu aiki a cikin wurin dake da qura ko yawan hayaqin ababen hawa harma da tarin HIV.

5.Basir da tsutsar ciki mai sanya ciki qugi da yawan kumburi ko tusa akai akai.

6.Ciwon hakora.Sai a tafasa da kyau a sha,a kuma sanya gishiri kadan a ciki a kurkure baki da ruwan.

7.Yana wanke mahaifa bayan haihuwa.

8.Yana karawa uwa lafiya da sanyata cin abinci da kuma samun yawan ruwan nono,sai a sha a cikin yoghurt.

9.Yana maganin dafin cizon qwari kamar maciji kunama,tsutsa,harma da karnuka sai a hada da qayar raqumi a ciki a tafasa sai a qona jar kanwa a saka 'yar qarama a ciki sai a sha nan take za a amaiye dafin da ikon Allah.

10.Waraka ga macen da ta haihu ko ta sha wahala wajen naquda a lokacin haihuwa sai a dake KIMBA a dibi rabin karamin cokali a saka ga nono ko yoghurt marar tsami a sha,ko a tafasa a sanya Zuma a sha.

11. kaikayin fatar jiki a saka ga fura ko nono a sha.

12. Tazarar haihuwa za a gauraya babban cokali na garin kimba da garin wannan maganin rabin cokali na __________sai a tafasa a sha Jim kadan bayan saduwa to ciki bazai shiga ba,amma fa ko yaushe aka sadu a dole sai an sha.Yana kawo jinkirin al'ada a wasu lokuta da kuma bacci a sanda a ka sha,amma duka wannan baya na nufin wata matsala bace.Ba zamu fadi wannan faidar ba ganin musibun wannan zamanin.Allah ya keuta

13.Daidaita sukari a cikin jini musamman mai fuskantar barazanar kamuwa da ciwon suga,ba za sha da yoghurt ko Zuma ba,za a tafasa a sha kawai a duk bayan kwana biyu.

14.Yana kare abinci ko abinsha daga lalacewa yana kuma kashin wasu kwayoyin cuta.Shi yasa ake saka shi ga nono ko fura ko wani magani.

15.Ana daka KIMBA qwara daya da citta qwara uku a sanya a cikin ruwan zafi na lemun tsami da Zuma da aka tafasa sai a sha,yana maganin cushewar ciki da hanji.sai a kula yana sanya gudawa.

16.Ana daka kimba da ganyen bagaruwa a cikin garin gero ayi gumba a saka nono mai kyau a dama a sha,maganin gyambon cikin daya tsananta.

17 Rage nauyin ciki dana jiki.

18.Maganin kaikayin fata da ido.

19.Maganin hawan jini,sai a saka a cikin so6o a tafasa a tace a gyara a zanka sha.

20.Karin ruwan maniyi ga namiji sai a gauraya da garin aya ko dabino a saka madara a sha.

Muna sane da masu yi mana copy and editing zuwa shafukansu da hada video na YouTube ana neman kudi da rubuce rubucenmu,mun barsu da Allah,Allah ya saka mana.

SHERE TO YOUR FRIENDS.

 A Kula ko wace matsala da yanda ake sha mata maganin,wata matsalar da yoghurt za a sha ,wata kuma da ruwan zafi,wata kuma da Zuma,wata kuma 
da nono.

1 Comments

Post a Comment