🍃🌼
KYAUTATAWA ALLAH ZATO
Sahabi Abi Huraira ya ruwaito daga Manzon Allah cewa: "Allah madaukakin sarki yana cewa: Ina nan a'inda bawana ke zato na, idan ya yi zaton alkhairi to wa kansa, hakanan idan ya yi zaton sharri to wa kansa"
صحيح الترغيب ٣٣٨٦
Abul Abbas AlQurduby Allah ya masa rahama yake cewa akarkashin wannan hadisin "Malamai sun yi sabani akan ma'anar wannan magana, suka ce: Ai zaton amsa addu'a alokacin da bawa ya rokeshi wasu kuma suka ce zaton karbar tubansa alokacin da ya tuba wasu suka ce zaton yi masa gafara alokacin da ya yi istigfari wasu suka ce *zaton karbar ayyukansa alokacin da ya aikatasu abisa sharrudan yinsu, yana Mai gaskata alkawarin Allah da kuma girman falalansa
Ni kuma na ce (Al-Qurduby ya ce): "Abunda zai karfafa wannan shi ne fadin manzon Allah "ku roki Allah kuna masu yaqinun za'a karba muku".
الترمذي ٣٧٢٥
Zaurenfisabilillah