WANE IRIN GROUPS KAKE CIKI A SOCIAL MEDIA?
GABATARWA:
Hausa Islamic Pictures Quotes.
-
🍂Wasu sukan shiga groups na addinin musulunci domin su ƙaru su kuma faɗaku, suji wa'azi ko su karanta nasiha mai matuƙar ratsa zuciya domin su ƙara kusanci ga ubangijinsu Allah, wanda hakan kuma zai iya zame musu farin ciki a ranar lahira.
-
🍂Wasu sukan shiga groups na siyasa ne domin su yabi wanda suke so ko kuma su caccaki abokin hamayyarsu, wanda hakan kuma zai iya zame musu nadama a ranar ƙiyamah.
-
🍂Wasu sukan shiga groups ɗin batsa ne domin su bawa idanunsu abinci ta hanyar kallon haramun, wanda hakan kuma zai iya zame musu asara da nadama a ranar lahira.
-
🍂Wasu sukan shiga groups ɗin fina-finai da comedies ne domin su sami nishaɗi da farin ciki, sun manta da cewa lallai babu wani alkhairi acikin duk wani jin daɗin da aka manta da Allah acikinsa.
-
"Dukkanin mu bayin Allah ne, kuma dukkanin mu masu yin kuskure ne, wanda yaji ko yaga kuskurensa kuma ya gyara shi, to haƙiƙa wannan shine yake da raubata, wanda kuma yaji ya gani ya sani sannan kuma ya wofuntar dashi, to lallai wannan sai yayi nadama a gaban Allah buwayi.
-
"Dukkanin wani groups ɗin da kake cikinsu, matuƙar kasan bazasu tunatar dakai lamarin Allah ba, to wallahi wannan mashiriricin group ne, kuma kayi gaggawar fita daga cikinsa kafin mutuwa ta riske ka, domin wallahi sai Allah yayi maka hisabi abisa duk irin groups ko pages ɗin da kake cikinsu a social media, gyara ya rage naka a yanzu.
-
Yaa Allah kasa mu zamto daga cikin datattun bayin ka waɗanda da zarar sunga kuskurensu suke ƙoƙarin gyarawa nan-take, Ameen.
-
✍🏿Hausa Islamic Pictures Quotes