YA KAI ƊAN UWA MUMINI

YA KAI ƊAN UWA MUMINI 



Idan kana so ka zama cikakken Mumini mai daraja awajen Allah, sai kayi ma jikinka da zuciyarka ado da abubuwa guda bakwai kamar haka:

1. Ka Qawata harshenka da faɗin gaskiya ako yaushe, ako ina, kuma ko akan waye. Allah yana cewa:

"YA KU MASU IMANI, KU KASANCE TSAYAYYU BISA ADALCI, KUMA MASU BADA SHAIDA DA GASKIYA, KO DA AKAN KANKU NE. KO KUMA IYAYE, KO MAKUSANTA. IDAN MA SUN ZAMANTO MAWADATA KO MATALAUTA, TO ALLAH SHINE MAFI CHANCHANTA DASU. KADA BIN SON ZUCIYA YA HANAKU YIN ADALCI.. ".
(Suratun Nisa'i ayah ta 135).

Kuma Allah yace : "YA KU WAƊANDA SUKAYI IMANI! KUJI TSORON ALLAH KU KASANCE TARE DA MASU GASKIYA".
(Suratut Taubah ayah ta 119).

Kuma Allah yana cewa:

"YA KU WAƊANDA SUKAYI IMANI, KUJI TSORON ALLAH, KU RIKA FAƊAR ZANCE NA GASKIYA".
(Suratul Ahzaab ayah ta 70).

2. KUNYA DA TAUSAYI A IDONKA : 
*******************************
Kunya ita ce adon Imani. Duk wanda bashi da kunya, to lallai bashi da imani. Hakanan tausayi shima yana daga cikin halayen Muminai. Manzon Allah (saww) yace : "KUNYA TANA DAGA CIKIN IMANI". 

Kuma yace "MASU TAUSAYI SUNE KAƊAI ALLAH YAKE TAISAYINSU DAGA CIKIN BAYINSA".

3. TAIMAKO AKAN HANNUNKA : 
*****************************
Duk wanda ya taimaki wani, to shima Allah zai taimakeshi. Hakanan duk wanda ya taimaki addinin Allah, to Allah zai taimakeshi kuma zai kiyayeshi daga afkawa cikin wuta, aranar tsallaka siradi. 

Allah yana cewa:

"IDAN KUKA BAMA ALLAH RANCHE, RANCHE MAI KYAWU, ZAI NINNINKA MUKU KUMA ZAI GAFARTA MUKU.. ".

Taimakon Marayu da miskinai da masu Qaramin Qarfi yana daga cikin hanyoyin samun ceto aranar lahira. Kuma masu yin sadaqah domin Allah, suna daga cikin waɗanda zasu zauna a karkashin inuwar Allah aranar da babu wata inuwa sai tasa. 

4. MURMUSHI DA SAKIN FUSKA :
******************************
Murmushi da sakin fuska shima yana daga cikin hanyoyin samun Garabasar lada mai yawa awajen Allah. 

Manzon Allah (saww) yace "KADA KA RAINA WANI ABU DAGA CIKIN AIKIN ALKHAIRI. KODA HAƊUWA DA ƊAN'UWANKA NE DA SAKAKKIYAR FUSKA".

Shi kansa yin murmushi ga Mumini sadaqah ne. 

5. SOYAYYA A ZUCIYA :
********************
Ka kudurce Son Allah da Manzonsa (saww) da soyayyar Salihan bayin Allah azuciyarka. Domin aranar lahira soyayya tana daga cikin manyan abubuwan da zasu fi yin amfani. 

Daga cikin dukkan ayyukan lada, babu abu mafi tsada kamar Son Manzon Allah (saww) da ahalin gidansa. Shi yasa ma yace : "IMANIN 'DAYANKU BA ZAI TABBATA BA, HAR SAI YAFI SONA FIYE DA DUKIYARSA DA 'YA'YANSA DA DUKKAN MUTANE BAKI ƊAYA".

Kuma yace : "KUSO ALLAH SABODA NI'IMOMINSA DA YAKE ZUBOWA AGAREKU. NI KUMA KU SONI SABODA SOYAYYAR DA KUKE YIWA ALLAH. SANNAN KUSO IYALAN GIDANA SABODA SOYAYYATA".

Wajen Soyayyar Muminai kuwa yace "BA ZAKU SHIGA ALJANNAH BA, HAR SAI KUNYI IMANI. KUMA BA ZAKUYI IMANI BA, HAR SAI KUN SO JUNANKU...".

6. TAWADHU'U DA TSORON ALLAH :
*********************************
Tawadhu'u tare da jin tsoron Allah afili da boye, sune ainahin halayen bayin Allah na kwarai. Girman kai da Taqama da dukiya da Fajirci sune halayen manyan kafirai irin su Fir'auna da Qaruna dasu Abu Jahl.

Shi yasa Allah yace "ALLAH YANA YIN AZABA GA DUKKAN WANI MAI GIRMAN KAI, MAI ZALUNCI".

Shi girman kai bashi da wata fa'idah koda awajen masu yinsa. Farkonka Maniyyi ne, Qazanta. Karshenka kuma Mushe ne mai wari. Duk abinda ka samu kuma anan duniya zaka barshi. 

Kuma babu bambanci tsakanin Qabarinka da na Talakan da bai ta'ba rike naira guda ba. To menene abun yiwa girman kan? 

7. HAKURI DA JURIYA WAJEN BIN ALLAH :
****************************************
Idan ka tsaya akan hanyar Allah, to dole sai kayi fama da shaitanun fili da na boye. Ba zasu ta'ba saurara maka ba, har sai sunga sun rabaka da hanyar Allah. 

Dole sai ka hadiye kwadayinka ta bangaren son duniya, da kuma bin sha'awar zuciyarka. Kuma ka toshe kunnuwanka daga zargin masu zargi. Kuma ka toshe idanuwanka daga kallon duk abinda Allah ya haramta maka.

Allah ya taimakemu ameeen thumma ameeen. Wannan nasiha ce daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP (July 14 2016) Shawwal 09 1437.
Post a Comment (0)