AL-AQEEDA AL-ISLAMIYYA 03



AL-AQEEDA AL-ISLAMIYYA 
_

Rubutu (03)

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

✿ Kuma babu wani ganye da zai fadi face da saninsa (Allah), hakanan kuma babu wata qwaya da take cikin duhun kasa, busash-shiya ce ko danya ce face tananan acikin littafi mabaiyani, Shi yana nan ya daidaita abisa Al-Arshi, mala'iku suna kewaye da shi.

✿ Kuma yana da sunaye mafiya kyawu da siffofi madaukaka, yana nan bai gushe ba tare da sunayensa da siffofinsa, ya daukaka ya girmi ace siffofinsa halittattu ne ko kuma ace sunayensa qagaggune.

✿ Ya yiwa Annabi Musa magana da maganarsa wacce take sifface ga zatinsa, ba wai halitta bace daga cikin halittunsa, kuma ya bayyana akan dutse sai ya zama gari saboda girma da buwaya na ubangiji.

مقدمة ابن زيد القيرواني لكتابه الرسالة...

#Zaurenfisabilillah

TELEGRAM:
 https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/

3/9/2020
___
Post a Comment (0)