BABU HADISI INGANTACCE AKAN YAWAN KWANAKIN HAILA
TAMBAYA❓
:
Assalamu alaikum
Na karanta amsar da malam ya bada wadda ban fahimce taba, Abusa tambayar da akayi mashi. Ta zuwan jini duk sati tare da cewa taje asibiti Amman sunce saidai tayi hakuri in na fahimci tambayar .
Hukncin matar da take da irin wannan lalora shine : Zata bar salla a duk lokacin da jini yazo mata in lokacin yin al'adattane ko da ya doge harfiye da kwanakin da takeyi mutukar bewoce kwana(15) ba, Amman in ya woce haka zatayi wanka tayi salla don haila ba ta wuce kwana(15).
:
AMSA👇
:
Wa'alaykumussalam
Abin da abokina ya fada shi ne fatawar Malikiyya da Shafi'iyya, saidai babu ko hadisi É—aya da ya tabbata akan cewa : jinin haila ba ya wuce kwana sha biyar, duk hadisan da suka zo akan haka ba su inganta ba, daga ciki akwai hadisin da aka rawaito cewa: "An tambayi Annabi s.a.w game da tawayar addinin mace, sai ya ce: "ÆŠaya daga cikinsu zata zauna rabin rayuwarta ba ta sallah"
Ibnul Jauzu ya raunana shi a littafinsa Attahkik 1\263 haka Annawawy shi ma ya ce: hadisin karya ne, kamar yadda ya zo a AlMajmu''u 2\405,
Ibnu Abdulhady shi ma ya raunana shi a cikin Tankihu attahkiki1\414, Baihaki a cikin Ma'arifatu assunan wal-athar,2\145 yana cewa: Na nemi hadisin da sanadi a littattafan hadisi amma ban taba ganinsa ba,
Haka nan Hanafiyya sun tafi akan cewa : Jinin haila ba ya wuce kwana goma, saidai duk hadisan da suka kafa hujja da su babu ingantacce a ciki, Duba Al-ilal Al-mutanahiyah na Ibnu Al-jauzy 2\382.
Zance mafi inganci shi ne haila ba ta da wasu kwanaki na musamman, kamar yadda sheik Ibnu Uthaimin ya tabbatar da haka a littafinsa na Dima'uddabi'iyya, tun da Allah da manzonsa sun rataya hukunce-hukuncenta ne da samuwarta, don haka duk inda aka samu jinin haila da sifofinsa (baki, karni) hukuncinta yana tabbata, saidai idan ya kasance mafi yawan rayuwa ko dukkanta, a lokacin ne zai zama jinin cuta.
Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaÉ—a wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH