FALALAR YIN SADAKA GUDA

FALALAR YIN SADAKA  


1) ALLAH YANA HORE AL'AMARIN MASU BADA SADAKA CIKIN SAUKI. 

Allah (Swt) ya fada a cikin Alqurani mai girma Cewa,
ﻓﺎﻣﺎ ﻣﻦ ﺍﻋﻄﻲ ﻭﺍﻟﺘﻘﻲ ﻭﺻﺪﻗﻲ ﺏ ﺍﻟﺤﺴﻨﻲ ﻓﺴﻨﻴﺴﺮﻩ ﻟﻠﻴﺴﺮﺍ ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﻠﻴﻞ ‏( ﺍﻟﻴﻞ : 5 )

Ma'ana
"Duk Wanda ya bayar kuma yaji tsoro kuma ya gaskata kyakyawan (kalma) to da sannu zamu saukake masa har ya kai ga samun sauki"

2) ALLAH ZAI NUNKA MA ABINDA KA BAYAR NINKI BA NINKIN. Haka Qurani yace,

ﻣَﺜَﻞُ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﻨْﻔِﻘُﻮﻥَ ﺃَﻣْﻮَﺍﻟَﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻛَﻤَﺜَﻞِ ﺣَﺒَّﺔٍ ﺃَﻧْﺒَﺘَﺖْ ﺳَﺒْﻊَ ﺳَﻨَﺎﺑِﻞَ ﻓِﻲ ﻛُﻞِّ ﺳُﻨْﺒُﻠَﺔٍ ﻣِﺎﺋَﺔُ ﺣَﺒَّﺔٍ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻳُﻀَﺎﻋِﻒُ ﻟِﻤَﻦْ ﻳَﺸَﺎﺀُ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﺍﺳِﻊٌ ﻋَﻠِﻴﻢٌ ‏( ﺍﻟﺒﻘﺮﺓ : 261 )
Ma'ana,
"Misalin Wadanda suke ciyar da dukiyoyin ta hanyar daukaka hanyar Allah, kamar misalin kwayar hatsi ce aka shuka tafitar da zangarniya guda bakwai cikin kowace zangarniya akwai kwayar hatsi guda dari, kuma Allah yana ninkawa ga wanda yaso, kuma Allah mai yalwatawane masani. (Suratul baqra 261).

3. TANA TOSHE KOFOFI GUDA SABA'IN NA SHARRI.

ﻗﺎﻝ ﺇﻣﺎﻡ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﻓﻲ ﻣﻌﺠﻢ ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ :
4402 - ﺣَﺪَّﺛَﻨَﺎ ﻋُﺒَﻴْﺪٌ ﺍﻟْﻌِﺠْﻠُﻲ، ﺛﻨﺎ ﺟُﺒَﺎﺭَﺓُ ﺑْﻦُ ﺍﻟْﻤُﻐَﻠِّﺲِ، ﺛﻨﺎ ﺣَﻤَّﺎﺩُ ﺑْﻦُ ﺷُﻌَﻴْﺐٍ، ﻋَﻦْ ﺳَﻌِﻴﺪِ ﺑْﻦِ ﻣَﺴْﺮُﻭﻕٍ، ﻋَﻦْ ﻋَﺒَﺎﻳَﺔَ ﺑْﻦِ ﺭِﻓَﺎﻋَﺔَ، ﻋَﻦْ ﺭَﺍﻓِﻊِ ﺑْﻦِ ﺧَﺪِﻳﺞٍ، ﻗَﺎﻝَ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ : ‏« ﺍﻟﺼَّﺪَﻗَﺔُ ﺗَﺴُﺪُّ ﺳَﺒْﻌِﻴﻦَ ﺑَﺎﺑًﺎ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺴُّﻮﺀِ »
Ma'ana
Manzon Allah (Saww) Yace, sadaka tana toshe kofofin sharri guda saba'in. (Sahih, Imamu DABARANI ne yaruwaito acikin littafinsa MU'UJAMIL L–KABIR: 4402).

4. MALA'IKU SUNA YI WA MAI YIN SADAKA ADDU'A

ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻋﻂ ﻣﻨﻔﻘﺎ ﺧﻠﻔﺎ ﻭﺍﻋﻂ ﻣﻤﺴﻜﺎ ﺗﻠﻔﺎ . ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ
Ma'ana
"Ya ubangiji ka mayar da abinda aka ciyar, kuma ka ɓata abinda aka riƙe". (Bukhari1442, Muslim 1010).

(5) SADAKA TANA KANKARE ZUNUBAI

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﻭﺍﻟﺼﺪﻗﺔ ﺗﻄﻔﻲﺀ ﺍﻟﺨﻄﻴﻌﺔ ﻛﻤﺎ ﻳﻄﻔﻲﺀ ﺍﻟﻤﺎﺀ ﺍﻟﻨﺎﺭ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ : 1242

Manzon Allah (Saww) yace, sadaqa tana kankare kuskure kamar yadda Ruwa yake kashe wuta.(sahihutargib 1242).

(6) ITACE INUWAR MUTUM RANAR QIYAMA:

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻇﻞ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﺻﺪ ﻗﺘﺘﻪ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ 872:

Manzon Allah (Saww) yace: Inuwar mutum ranar Qiyama Sadaqan sa (Sahihut targib: 872 )

(7 (TANA KARE AZABAN QABARI:

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺇﻥ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ ﻟﺘﻄﻔﻲﺀ ﻋﻦ ﺍﻫﻠﻬﺎ ﺣﺮ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ : 1251

Manzon Allah (Saww) yace: Sadaqa tana kashe zafin Qabari ga mai ita. (sahihut targib 1251)

(8) TANA KARE AFKAWAN MASIFA:

ﻋﻦ ﺃﻧﺲ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﺻﻨﺎﺀﻉ ﺍﻟﻤﻌﺮﻭﻑ ﺗﻘﻲ ﻣﺼﺎ ﺭﻉ ﺍﻟﺴﻮﺀ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ : 3795

Manzon Allah (Saww) yace: aikata abin kirki yana kare afkawan musiba . (sahihuJami’ussagir: 3795 )

(9) TANA MAGANIN CIWO:
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺩﺍﻭﻭﺍ ﻣﺮﺿﺎﻛﻢ ﺏ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ 3357:
Kuyi jinyan marasa lafiyanku da sadaqa (Sahihu jami’u 3357)

(10) TANA HUCE FUSHIN ALLAH
ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺇﻥ ﺍﻟﺼﺪ ﻗﺔ ﺍﻟﺴﺮ ﺗﻄﻔﻲﺀ ﻏﻀﺐ ﺍﻟﺮﺏ ﺗﺒﺎﺭﻙ ﻭﺗﻌﺎﻟﻲ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ 888:
Manzon Allah ﷺ yace: lallai sadaqan ɓoye tana huce fushin Ubangiji mai albarka da ɗaukaka. ( sahihut targib 888:)

(11) TANA KAREWA DAGA WUTA :

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﻓﺎﺗﻘﻮ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﻭﻟﻮ ﺑﺸﻖ ﺗﻤﺮ . ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ
Manzon Allah ﷺ yace: kukiyayi wuta kada da tsagin dabino. (Bukhari 1413, Muslim 1016)

(12) BATA RAGE YAWAN DUKIYA:

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﻣﺎ ﻧﻘﺺ ﻣﺎﻝ ﻣﻦ ﺻﺪ ﻗﺔ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ‏( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ 1249: )
Manzon Allah ﷺ yace: Sadaqa bata rage dukiya.( sahihut-targib 1246)

(13) TANA LAUSASA BUSASHIYAR ZUCIYA

ﻋﻦ ﺍﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ : ﺍﻥ ﺭﺟﻼ ﺷﻜﺎ ﺇﻟﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ , ﻗﺴﻮﺓ ﻗﻠﺒﻪ . ﻓﻘﺎ ﻝ " ﺍﻣﺴﺢ ﺭﺍﺱ ﺍﻟﻴﺘﻴﻢ , ﻭﺍﻃﻌﻢ ﺍﻟﻤﺴﻜﻴﻦ . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺣﻤﺪ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ‏( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ 3679: )

Abu huraira (rta) yace wani mutum ya kawo kukan bushewar zuciyarshi ga Manzon Allah ﷺ sai yace masa:” ka shafa kan maraya kuma kaciyar da miskini” ( sahihut-targib 3679)

(14) TANA KARE MUTUNCI:

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﺫﺑﻮﺍ ﻋﻦ ﺍﻋﺮﺍﺿﻜﻢ ﺏ ﺍﻣﻮﺍﻟﻜﻢ . ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ 3425:

Manzon Allah ﷺ yace: ku kare mutuncinku ta hanyar dukiyanku. (Sahihu jamiu 3425).

Yaa Allah ka hore mana Abinyin sadaka kuma ka hore mana zuciyar bayarwa.

TELEGRAM CHANNEL
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)