HUKUNCIN SAUKE ALQUR’ANI DOMIN CIN JARABAWA:
TAMBAYA❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.
Ina hukuncin ɗaliban jami’a su haɗu su sauke Alqur’ani, su yi tawassuli da shi don neman su ci jarabawa?
AMSA A143:
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
[1] A asali yin addu’a ga Allaah, da roƙon sa a cikin kwaɗayi da tsoro don neman biyan buƙata a cikin al’amura kyakkawan abu ne a cikin shari’a. Akwai nassoshi masu yawa a cikin Alqur’ani da Sunnah Sahihiya da suka yi nuni ga haka, kamar haka:
Kuma Ubangijinku ya ce: Ku yi addu’a gare ni zan amsa muku. (Surah Ghaafir: 60)
Da kuma:
Kuma ku yi addu’a ga Ubangijinku a cikin ƙanƙan-da-kai kuma a ɓoye. (Surah Al-A’raaf: 55)
A cikin hadisin da At-Tirmiziy: 3232 ya riwaito kuma ya ce: Kyakkyawa ne ingantacce, Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
ﺍﻟﺪُّﻋَﺎﺀُ ﻫُﻮَ ﺍﻟْﻌِﺒَﺎﺩَﺓُ
Addu’a ita ce ibada.
Don haka, wajibi ne ga musulmi ya riƙe wannan aikin ibadar a ko yaushe, kuma a kan komai, ya zama mai yawaita addu’a ga Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala, domin neman samun biyan buƙata.
Haka nan kuma yin tawassuli da karatun Alqur’ani domin neman biyan buƙata a wurin Allaah shi ma abu ne mai kyau. A cikin Surah Al-Ma’idah: 35, Ubangiji Ta’aala ya ce:
Ya ku waɗanda suka yi Imani! Ku ji tsoron Allaah, kuma ku nemi tawassuli (tsani zuwa) gare shi.
Kuma malamai sun yarda cewa ana yin tawassuli ga Allaah ne ta fuskoki biyu:
(i) Ko dai da Siffofi da Sunayen Allaah Ta’aala.
(ii) Ko kuma da Ayyukan ibada da Allaah ya ɗora wa bayinsa.
Alqur’ani kuwa bayan kasancewarsa Siffar Allaah Ta’aala Maɗaukakin Sarki, kuma karatunsa babban aikin ibada ne da Allaah ya ɗora wa bayinsa. Tun da kowane harafi aka karanta lada goma ake samu, kamar yadda hadisai suka yi bayani kuma kowa ya sani.
Sai dai kuma surar yadda waɗannan ɗalibai suka zo da shi na yin karatun da tawassulin a ƙungiyance shi ne ban san madogarinsa ba. Kuma kamar yadda malamai suka yi bayani, shi ɓangaren ibada a cikin addinin nan ba kamar ɓangaren mu’amala ba ne. A nan ana tsayawa ne kawai ga abin da nassi ya yi umurni, ba a yin komai sai abin da shari’a ta nuna kawai.
To, don gudun kar su kauce wa wannan ƙa’idar kuma a samu matsala, da sai kowannensu kawai ya yi amfani da duk wani aikin alheri na ibada da yake iyawa, kamar nafilolin sallah, ko azumi, ko sadaka, ko biyayyar iyaye, ko sada zumunci, ko tilawar Alqur’ani, ko zikiri maiyawa, da sauransu, sannan ya samu lokacin da ya dace - kamar ƙarshen dare, lokacin da Ubangiji Ta’aala yake saukowa zuwa saman duniya - ya roƙi Allaah buƙatarsa da ta ’yan uwansa. Ko kuma dukkansu su nemi iyayensu su riƙa yi musu addu’a a kan haka, tun da dai addu’o’in iyaye ga ’ya’yansu karɓaɓɓu ne, kamar yadda hadisi ya nuna. Ko kuma su samu wani limami mutumin kirki ya yi musu addu’a a lokacin da ya dace, kamar a lokacin huɗuba a masallacin Jumma’a, kamar yadda ya zo a cikin hadisi a babin addu’ar roƙon shayarwa.
Amma kuma kar a manta: A nan addu’a kaɗai ba ta ci, dole sai ɗalibai sun haɗa da halartan darussa malamai ko lakcarori tun farko; da yawaita yin bitan karatun don samun ƙarin fahimta; da kuma bitan takardun jarabawan da suka gabata tun kafin ranar jarabawa, da dai sauransu.
Allaah Ta’aala ya datar da muga abin da yake so kuma yake yarda da shi a cikin zantuka da ayyuka.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Don Allah Yan'uwa Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING, wasu da yawa zasu amfana.