HUKUNCIN ƊAURA AURE TA HANYAR SADARWA (Social Media)
TAMBAYA❓
:
Shin ko ya halatta a daura aure ta hanyar magana a wayar salula idan ya kasance ba a gari guda matar da mijin suke zaune ba?
:
AMSA👇
:
Farko dai daga cikin rukunan ɗaura aure akwai furta lafazin bayarwa da kuma karɓa tsakanin waliyyin amarya da kuma ango ko wakilin ango. Malamai sukace sharaɗi ne ya kasance mai bada aure da mai karɓar aure su kasance a majalisi ɗaya suke zaune.
Sai dai Malamai na wannan zamanin sunyi saɓani dangane da hukuncin ɗaura aure ta hanyar kafafen sadarwa na zamani kamar ta hanyar internet ko ta wayar salula da makamancinsu. Wasu daga cikin Malamai sukace a'a bai halatta ba, saboda a kare martabar auren, domin kuwa ana iya amfani da wannan hanyar ya kasance ba asalin waliyyan matar ba ne suka ɗaura auren wasu ne kawai dabam, dan haka kenan yaudara za ta iya shigowa ciki lamarin, domin ana iya kwaikwayon muryar wani mutum ayi amfani da ita a matsayin cewa shi ne waliyyin matar, dan haka sukace abinda yafi zaman lafiya shi ne kawai a nisanci hakan saboda a tsare martabar farjin ma'auratan, ko kuma a wakilta wani Mutum a can ya zama shi ne wakilin ango.
To amma a gefe ɗaya kuma akwai Malaman da suke ganin cewa ya halatta a ɗaura aure ta hanyar magana a wayar salula idan ya kasance an aminta daga dukkan wani ruɗani ko yaudara da kan iya shigowa cikin lamarin. Malaman sukace idan yazama an cika dukkan sharuɗɗan aure to ya halatta a ɗaura aure ta hanyar magana a wayar salula, amma ya kasance akwai tabbas ɗin cewa waliyyin amarya ne yayi maganar ba da auren.
Sharaɗi na gaba kuma ya kasance a ƙalla akwai shaidu guda biyu da sukaji maganar da kunnensu cewa waliyyin amarya ya bada aure shi kuma ango ko wakilin ango ya karɓa, idan akayi haka to aure ya tabbata.
Dan haka dai magana mafi inganci kamar yadda Malamai da yawa suka rinjayar itace, sukace kamar yadda ya inganta a ɗaura aure ta hanyar aika rubutu a jikin takarda, wato (wasiƙa) idan sharuɗɗan amfani da hakan sun cika, to haka nan ya halatta a ɗaura aure ta hanyar kafofin sadarwa kamar Internet ko magana a wayar salula, idan ya kasance dukkan sharuɗɗan da ake buƙata sun cika, Musamman kuma ace yakasance anyi amfani ne da irin Na'urar da za ta riƙa nuna Videon Mutum a lokacin da yake magana.
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'α'αʟα
Mυѕтαρнα Uѕмαn
08032531505
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH