WANENE JARUMI RAJESH KHANNA?
An haifi Rajesh Khanna a shekara ta 1942 inda ya mutu a shekara ta 2012.
Asalin sunansa shine Jatin Khanna sanadiyar shigowarsa Bollywood ya koma Rajesh Khanna. Ana kiransa da sunaye irinsu Kaka da First Superstar.
A shekara ta 1966 ya fara film inda ya fara fitowa a wani film me suna Aakhri Khat.
Daga shekara ta 1969 zuwa 1971 Rajesh Khanna ya kafa wani Record Wanda shi kadai ne me irin wannan Record. Rajesh Khanna yayi finafinai guda 15 a jere amma duk ciki babu kasa da Semi Hit Kuma cikin shekaru 3.
1. Bhadan (1969) Hit
2. Doli {1969) Semi Hit
3. Aradhana (1969) Blockbuster
4. Do Rasste (1969) Blockbuster
5. Kati Patang (1970) Blockbuster
6. The Train (1970) Hit
7. Safar (1970) Hit
8. Saacha Juhtha (1970) Super Hit
9. Aan Milo Sajna (1979) Super Hit
10. Aanand (1970) Hit
11. Haathi Mere Saathi (1971) Blockbuster
12. Amar Prem (1971) Semi Hit
13. Andaz (1971) Hit
14. Maryada (1971) Hit
15. Dushman (1971) Super Hit
Wannan shine Record din Rajesh Khanna cikin shekaru 3, a cewar Boxofficeindia wannan itace nasara mafi girma da Jarunmin India ya taba ganin irinta a tarhin Hindi Cinema. Shine ruling mafi girma a tarhin Bollywood. Rajesh Khanna Saida ya shafe shekaru 17 yana matsayin wanda yafi kowanne jarumi tsada a Bollywood.
KARFIN STARDOM
Idan ana maganar Stardom a tarihin Bollywood dazarar an ambaci sunan Rajesh Khanna to anje bango. Shine jarumin da ba a taba jarumi mai farinjininsa ba a Bollywood.
Anyi lokacin da idan Rajesh Khanna zaiyi taro to ko Shugaban kasar India baya taro a ranar saboda yasan baza a cika ba. Shi kansa Shugaban kasar India idan zaiyi taro anaso a cika saiya gayyato Rajesh Khanna.
Mutanan India suna mutukar kaunar Rajesh Khanna domin komai nasa Idan ya fita rububinsa suke uwa kudi. An nunawa Rajesh Khanna tsagwaron soyayya ta yadda duk inda ka ganshi saika ga dandazon mutane.
Wani jarumi ya taba wucewa ta kofar gidan su Salman Khan yaga taron mutane da suke jiran fitowar jarumi Salman Khan , jarumin ya kira Salim Khan a waya inda yake cewa naga taron mutane irin Wanda ban taba gani ba a kofar gidanka sunzo dun suga danka. Salim Khan yace masa ai shi yasha ganin fiye da haka a kofar gidan Rajesh Khanna alokacinsa.
A wata hira da wani dan jarida ya tambayi Salman Khan akan Rajesh Khanna, Salman Khan ya gargadi wannan dan jarida akan cewa ya daina hadashi da Rajesh Khanna domin 3 Khans basu da 10% daga cikin 100% na Stardom din Rajesh Khanna.
Dukda cewa Rajesh Khanna bai jima yana ruling ba amma yana da girman Stardom din da babu mai irinta a Bollywood. Sannan a iya shekarun uku daya shafe yana ruling itace best phase a tarihin Bollywood.
Saboda tsabar girman Stardom din Rajesh Khanna alokacin da yan kallo suka fara dawowa kallon finafinan Aamitabh Bachchan suka daina kallon na Rajesh Khanna Bollywood har rabuwa gida biyu tayi.
Wasu suna ganin lokacinsa ne ya wuce inda wasu suke ganin ai finafinan soyayya aka daina yayi.
Ana ganin girman Stardom irinta Rajesh Khanna ai tafi karfin ace karshensa ne yazo. Wannan yasa aka shirya masa manyan films na fada guda 6 amma abun mamaki dukansu faduwa sukai.
Daga wannan lokacin Aamitabh Bachchan ya fara nasa mulkin 👌👌👌👌