DA KAMALA TA.
"Mace mai kamala daban take acikin sauran mata, wasu suna amsa sunan su a matsayin mata, amma kuma ba kowacce bace take da cikakkiyar kamala wajen kare kanta da kuma mutuncin ta"
-
"Da yawan mata a gaban iyayensu ne kaɗai suke da kamala, amma da zarar sun fito waje, sai su watsar da kamala da kuma kamun kan da suke dashi a gaban iyayensu, da zarar sun fito waje sai suke bayyanar da tsaraicin su ga jama'a"
-
"Mace da dama za ka ganta a gaban iyayenta tamkar baya yin magana a rayuwarta, amma da zarar ta fito waje, sai kaji irin maganganu da baka yi tsammanin jin irin su daga gareta ba"
-
"Ki kasance a rayuwarki duk wanda zai soki to zai soki domin kamalarki ne, duk wanda zai ƙiki to zai ƙiki don kin kare kamalarki ne, kada ki bawa shaiɗanu ƙofar shiga zuwa gareki, lallai ki sani!, kare haƙiƙanin gangar jikinki yana daga alamun kare haƙiƙanin imaninki ne, sabida haka kamalarki itace mutuncin ki, kiyaye kamalarki tamkar kiyaye imaninki ne, kamala abace mai daraja a gareki, sabida haka ki kula da ita sosai kada ki zamto ballagaza"
-