DIREBA DA ƊANSANDA

DIREBA DA ƊANSANDA.


Wani dan sanda ne ya tsare direba, ga yadda tattaunawarsu ta kasance: dan sanda: “Ina takardun motarka?” Direba: “Ga su nan.” dan sanda: “Ina lasisinka?” Direba: “Ga shi nan.” (Komai aka tambayi direba yana da shi, dan sanda ya gaza kama shi da laifi). dan sanda: “To wa ya ce ka rika tafiya kai daya a mota, idan wani abu ya same ka wa zai maida ka gida?” Direba: “Manzon Allah (SAW) ya ba mu wata addu’a, a duk lokacin da zan yi tafiya, idan na karanta ta, mala’iku dubu suna tare da ni.” dan sanda: “Mala’iku dubu a karamar mota? To ka yi obalodi, mu tafi ofis, na kama ka!”
Post a Comment (0)