GATA DA KAMUN KAI DA TARBIYA AMMA TA RASA SAURAYI
TAMBAYA❓
.
Assalamu alaikum.malam Allah ya saka maka da mafificin alkairi, malam kawatace take cikin damuwa, damuwarta ta itace,ta kasance mace ce mai kamun Kai ga ilimi da tarbiyya,Amma Babu saurayin da yake zuwa gurinta gashi shekarunta sun Kai 25 shi ne abin yake damunta.kuma tana matukar San tayi aure,Sai Kuma take tunanin ko Don tayi digree ne shi yasa mazan suke Jin tsoron zuwa gurinta,Don Allah a tayata da addu'a._
.
AMSA👇
:
Tabbas Akwai irin Wannan Tunanin Na ta, Sabida da yawa Maza ba Sa Auren Macen da tayi Zurfin Karatun zamani. musamman Ma wadda take da Matsayin Karatu na degree.
Dalilin su shine. Duk wadda Aka Ce tana da degree, Lalle Zaka Samu Tana da wayewar da ta fi Karfin Tunaninsu.
Sannan Wasu Mazan Suna ganin Kamar idan mace ta yi Zurfi a Karatun zamani Kamar ba zata Yiwa Mijinta biyayya ba, Sabida zata na Kallon Sa a Rene Kamar ma Wanda bai Waye ba. Zatadinga ganin kamar Ita kadai ce wayayyiya. Shi bai Waye ba.
Sannan Wasu Mazan suna Ganin kamar wadda ta yi Zurfi a Karatun Zamani Dole Zaka Samu tayi gogayya da Maza Kuma ba bu Ranar da zata ta ba dena gogayya da Maza.
Sabida Nan Gaba ma Aikin Gwamnati zata Nema. Wanda kuma Kamar gogaggeniyar 'ya Mace Budurwa ko mai Aure tare da Maza, ya sabawa Tarbiyyar Musulunci.
Sannan wani Lokacin Zaka Samu Akasarin Matan da sukayi Zurfi a Karatun Zamani, Zaka Samu idan Suna Daukar Albashi. To fa Mijinta Ma bai isa ya gaya mata Magana ta dauka ba. Sabida Tana Samun kudi.
Sai dai Kuma duk Wadannan abubuwan da na zayyano Ba Lalle ba ne ka Samu Kowacce mace ce take da irin wannan Tunanin ba.
Amma dai Maza sukan Gujewa Mace ne Sabida Tunanin Faruwar ɗaya daga Cikin Wadannan Abubuwan da na Lissafo Miki.
Amma dai Tadinga yin Addu'a, insha Allah. Allah zai Kawo Mata Miji Kuma na Gari, Domin yanzu haka wannan zancen da Nake Yi miki. Zaki Samu wani Namijin Shi Kuma irin Wadannan Matan ya ke So Ma'ana wadda tayi Zurfi a Karatun Zamanin.
Amma dai Akasarin Maza ba su fiya son Irin Wadannan Matan.
Allah ta'ala yasa mudace
:
©✍🏽 Sadeeq Ñagogo{βluñgu}
:
_ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.