LUKUMAN DA SURAJO

LUKUMAN DA SURAJO


Wasu samari biyu LUKMAN da SURAJO na tafiya akan hanya, sai suka zo wucewa ta gaban wani gida mai bene. Wata kyakyawar budurwa ta leko daga window tana masu murmushi.

LUKMAN: kai SURAJO dubi wata kyakyawar yarinya can tana mana murmushi.

SURAJO: Hmm kyale ta kawai, zo mu tafi.
Har sunyi gaba sai LUKMAN ya kara waigowa, sai ta yi masa alamun zo da hannu.

LUKMAN: SURAJO tana kirana fa

SURAJO: ka kyale ta nace, zo mu tafi.

LUKMAN: kai ko anya ba bakin ciki kake min ba. Gaskiya sai naje.

Sai Lukman ya nufi gidansu yarinya, ta shigar dashi falo suka gaisa, ta kawo masa abinci da abinsha. Kafin ya fara cin komai sai suka ji mota ta tsaya. Budurwar ta leka window tace "ga mijina ya dawo". lukman ya tashi a tsorace yana neman hanyar fita sai yarinyar tace "zo kaga dauki kayan nan ka fara guga, in ya shigo zance mai guga ne na kira". Lukman ya kwashi tulin kaya ya cigaba da guga, ya kwashe ranar gaba daya yana guga kaya sunki karewa kuma mijin bai fita ba.

Da safe sai LUKMAN da SURAJO suka hadu a hanya.

LUKUMAN: hmm SURAJO kasan jiya wuni nayi ina guga a gidansu yarinyar nan kuwa.

SURAJO: ba nace maka kar kaje ba, duk KAYAN nan daka gani ni na wankesu shekarana iya...
Post a Comment (0)