MAGANIN ALJANUN SOYAYYA (JINNUL ASHIQ)

MAGANIN ALJANUN SOYAYYA (JINNUL ASHIQ).


TAMBAYA TA 2527
*******************
Assalamu Alaikum, dafatan Malam na lafiya, Amin. Malam na kasance tunda na taso lokutta kayyadadu ne da zance an zo zance wajena, duk wadanda nake haduwa da su da tafiya ta miqa sai mu rabu ba fada ba komi, sai inji sun fice mun daga rai, yanzu haka shekaru na ashirin da hudu, alamomin da dama sun bayyana cewa ina tare da jinnu saboda yawan mafarkin da nake, sannan ina son zaman kadaici ni kadai, magana ma bata dameni ba. Yawancin mafarkan ina na mace ne tana saduwa dani, ko na namun daji ko ina gudu, da yake ina yawan azkar sai ya kasance a mafarkin ina yawan cin nasara. Munje islamic Chemist an mun ruqya da magungunna na sha da shafawa amma har yanzu shiru, dan kwanakim nan ma mafarkin akuya, kadangare da maciji nayi. Sannan wani bawan Allah da ya ganni yana so bayan sallah nan, hankalina yayi matukar tashi har ya zamo da naga kiransa gabana zai ta faduwa, na kashe wayata ba tare da na qara sauraren shi ba.
Kullum cikin addu'a nake Allah ya yaye mun, idan akwai addu'ar da za a taimaka min da ita ina yi da kaina. Nagode Malam, Jazakallahu khair jaza'i

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Wadannan duk abubuwan da kika lissafa suna daga cikin manyan alamomin shafar Aljanin soyayya ( JINNUL ASHIQ). Kuma bayan haka zaki rika jin yawan fushi, faduwar gaba, jin kamar ana binki abaya idan kina tafiya, Qin shiga jama'a, Qaurace ma karatun Alqur'ani, kasala wajen yin zikirin Allah, etc.
Daga cikin hanyoyin da zaki bi domin Magance matsalar akwai :
1. Ki samu bokiti mai tsafta ki cikashi da ruwa sannan ki samo ganyen magarya guda bakwai ki dandakasu da dutse ki zuba acikin ruwan, ki tsoma babban yatsan hannun damanki acikin ruwan sannan ki karanta wadannan surori da ayoyin acikinsa :
- Fatiha.
- Ayoyi hudu na farkon baqara.
- Ayatul Kursiyyi tare da ayoyi 2 na gabanta.
- ayoyi uk7na karshen baqara.
- Ayoyi 10 na farkon Aali imran.
- Ayoyi 10 na karshen suratu Ibraheem (as).
- Suratul Hajji ayah ta 6 zuwa ta 15.
- Suratun Nuur daga farkonta zuwa ayoyi 4.
- Suratul Qamar baki dayanta.
- Ayoyi 10 na farkon suratut Tur.
- Suratu Yaseen Baki dayanta.
- Suratul Yaqteen (Sad) ayoyi 20 na farkonta.
- Suratuz Zukhruf.
- Suratul Mulk.
- Suratul Burooj.
- suratul feel.
- Ikhlas da Falaqi da Naas.
Kina yin karatin, numfashin karatun yana sauka akan ruwan.
To wannan ruwan zaki rika shansa har makonni 5 (35 days). Kada kisha wani ruwan sai shi kadai. Idan ya kusa Qarewa sai ki sake ha'da wani. Kuma kina shafawa ajikinki kullum sau biyu (safe da yamma).
Ki nemi Almujarrab na ZAUREN FIQHU domin magance yawan fushin da suke sanya miki, tare da juyar da tunaninki da sukeyi. Ki nemi MUHRIQUL JINNI na ZAUREN FIQHU shi kuma kina shafawa kullum kafin ki kwanta barci, domin magance saduwar da sukeyi dake.
Ki nemi Man Habbah da Man Zaitun ki tofa wadancan ayoyin acikinsa, ki rika cin abinci dashi har tsawon kwanaki 35 zuwa 41.
In sha Allahu aljanu ko sun kai dubu ajikinki zasu Qone, kuma zakiyi aurenki babu matsala in sha Allahu.
Don Qarin bayani ko neman shawarwari zaki iya tuntubar ZAUREN FIQHU akan wadannan lambobin 07064213990 08163621213 09094623006.

WALLAHU A'ALAM.
Post a Comment (0)