MAGANIN 'ULCER' HAR ABADA DA YARDAR ALLAH

MAGANIN 'ULCER' HAR ABADA DA YARDAR ALLAH



Daga Shafin Magunguna A Musulunci

Kamar yadda na yi alkawarin zan kawo maganin Ulcer Alhamdulillah yau na cika alkawarin ga sau fa'idoji nan guda biyu sai a jarraba,kuma insha Allah ana rabuwa da ita ne har abada 

ABINDA ZA A NEMA

1. Kabeji (Cabbege)
2. Lemon tsami (Lemon)
3. Zuma.

 Da farko zaka yanka kabejin naka kanana sai ka yi markada da ruwa kamar kofi daya sai ka zuba shi a kofi, sannan ka zuba lemon tsami kamar cokali daya, zuma cokali daya sai ka juya ka sha. Za ka yi haka sau biyu a rana.

HANYA TA BIYU 

ABINDA ZA A NEMA.

1. Garin hulba (FENUGREEK)
2. Lemon tsami ( Lemon)
3. Zuma

YADDA ZA A HADA 

 Da farko zaka tafasa garin hulbar naka da ruwa kofi daya bayan ka tafasa sai ka sauke idan ya dan wuce sai ka zuba lemon tsami Chokali 1 Zuma chokali 1 ka juya kasha,shima zakai haka sau biyu a rana.

Dukkan hanyar da zaka jarraba zakayi na tsawon kwana 15, insha Allah zaka rabu da Ulcer har abada.

Abin sadaqa a yi wa Annabi Salati.

Don Allah a yada domin karuwar jama'a.
✍ Alkulafa'urrashidun

1 Comments

Post a Comment