AL-AQEEDA AL-ISLAMIYYA 04

AL-AQEEDA AL-ISLAMIYYA 



Rubutu (04)

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

✿ Al-Qur'an maganan Allah ne ba halittarsa ba bare watarana ace ta halaka, ba kuma sifface ta abun halitta ba bare ace ta wanzu.

✿ Kuma imani da qaddara ta alkhairi da ta sharri, mai zaqi da mai daci duka wadannan Allah Ubangijinmu shi ne ya qaddara su, jujjuyawan lamuran yana hannunsa, tushensu kuma na daga hukuncin sa.

✿ Ya san komai kafin faruwarsa, komai na faruwa ne da qaddarawarsa, babu wani magana ko aiki da wani bawansa zai yi face ya hukunta faruwarsa kuma ya san da faruwarsa kafin ya faru. Allah na cewa: "Ku saurara shi wanda ya yi halitta ai masanine kuma shi ne wanda yasan abubuwan da suke boye kuma mai bada labarin su". (AlMulk 14).

مقدمة ابن زيد القيرواني لكتابه الرسالة...

#Zaurenfisabilillah
Post a Comment (0)