ZAMANTAKEWA TSAKANIN MAI GIDA DA MATANSA TANA TSAYAWA NE AKAN DORAN AL'ADAR DA BA TA SABAWA SHARIA BA

ZAMANTAKEWA TSAKANIN MAI GIDA DA MATANSA TANA TSAYAWA NE AKAN DORAN AL'ADAR DA BA TA SABAWA SHARIA BA


Tambaya:
السلام عليكم ورحمة الله 
وبركاته 
Mutum ne yake da mata biyu, yana tafiya da su aiki hajji da umara, to daya ta manyanta ta daina haihuwa, idan lokacin tafiyar yayi karamar tana da ciki zai iya tafiya da dayar?

Amsa:
Wa alaikum assalam wa rahmatullhi wa barakatuhu

Ana iya yin kuri'a kamar yadda Annabi (SAW) yake Yi idan zai yi tafiya, ko kuma su zauna da Mai gida su cimma matsayar da kowa zai gamsu da ita.
Galibin yanayin zamantakewar aure tsakanin Mai gida da matansa suna tsayawa ne akan doran al'adar da ba ta sabawa Sharia ba, kamar yadda Hadisai da yawa su ka Yi nuni zuwa lura da al'ada a lamuran aure da shayarwa da kuma ciyarwa, don haka duk Abin da suka cimma daidaito a tsakaninsu shi ne daidai.

Allah ne Mafi Sani

Dr. Jamilu Zarewa Hafizahullah 

28/10/2020
Post a Comment (0)