ABUBUWA 5 GAME DA YAƘIN RUSSIA DA UKRAINE
1- Lallai Allah yana yiwa Azzalumi talala har sai idan ya tashi kamashi to ba isa ya kubuce ba, Ukraine ta shiga gamayyar ƙasashen da suka taya America yaƙar Iraqi a 2003, sojojinta kuma sun fi na ko wacce ƙasa ƙazanta da rashin imani da ta'addanci akan musulmai bisa shaidar America kanta, sai ga shi yau Allah ya sallaɗa musu wasu azzaluman ƴan uwansu sun kuma rasa masu kawo masu ɗauki na gaske, lallai Annabi (SAW) ya yi gaskiya.
2- Ukraine darasi ce ga shuwagabannin musulmai da suke kwashe dukiyar al'ummarsu suna biyan America jizya da sunan neman kariya, indai har suka juyawa ƴan uwansu mabiya addininsu baya,bayan tilin alƙwawuran ba su kariya, da romon bakan za su tsaya musu, ina kuma ga musulmai?? Hakan kuma ta sha faruwa a tarihin America tun daga kan Faransa zuwa Kurdawa, da Muhammad Rida Bahlawi sarkin Iran, da Anwar Sadata har zuwa kan su Saddam su Gaddafi ga Ukraine nan ma ta shiga lissfai.
3- A yayin da shugaban ƙasar Ukraine yake ta mita cewa turawa sun juyamai baya, alhalin duk da cewa sun ƙi su ba shi cikakken taimako ne ta hanyar shiga yaƙin tare amma har yanzu suna ƙoƙarin taɓuka wani abu game da Russia ta hanyar siyasa da kuma tattalin arziki, suna kuma goyon bayansa, amma yake ta wannan mitar, anan ne zamu jinjina irin jihadi da ƙoƙarin da Afghanistan ta yi a 2001 yayin da aka barta ita kaɗai a duniya babu ko magana ɗaya ta nuna goyon baya balle wani mataki, hakanan Muslman Falasɗin musamman waɗanda suke Ghazza da na Syria da sauran ƙasashen musulmai, wannan zai nunama irin yanayin da musulman suka shiga sannan kuma zai nunama irin bambancin da ke tsakanin mumini wanda imaninsa shine makaminsa Ubangijinsa kuma shi ne gatansa shiyasa ma ba ya damuwa da wane bai taimakeshi wane ya juyamai baya, domin yasan cewa nasara a hannun Allah take, da kuma wanda ba musulmi ba wanda ya gama rataya komai nasa ga wani. Kwatanta jawabin shugaban Ukraine da jawabin Mulla Umar na Afghanistan a 2001 zaka ga bambancin Musulmi da kafiri.
4- Bayan Rushewar Tarayyar Soviet (USSR) a 1991 Ukrain da ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen wannan tarayyar ta wayi gari tana mallakar ɗaya bisa ukun makaman ƙare dangain duniya (Nuclear), amma haka ta tattara su ta ba wa Russia bisa shawarar America da kuma alƙawura na cewa za ta ba ta kariya ita kuma Russia ta yi alƙawuran cewa ba za ta yaƙeta ba, sai gashi yanzu ana ganin akasi, babban darasin anan shine iya wuya ba a rabuwa da makamin kare kai, domin mara ƙarfi ba shi da gata, iya ƙarfinka iya mutuncinka a duniya komin gaskiyarka indai kai mai raunine to a banza kake, daidaton ƙarfi shi yake kawo zaman lafiya ba wani abu ba, don duk wanda yasan cewa in ya taɓaka kana da abinda zaka rama to ba zai ma kuskuren taɓaka ba.
5- Mun daɗe mune ababen kallo a duniya duk jini da yake zuba a duniya namune duk wani shiri idan akan ƙullu a kanmu yake karewa, amma yanzu muma lokacin namu kallon yayin yayin da maƙiyanmu suka koma kan junansu, muna masu addu'ar su casu, da a ce ƙasashen musulmai suna masu cin gashin kansu da za su iya amfani da wannan rikici wajen su ga cinma wata maslaharsu.
#Abdurrahman Muhd Sani Umar
Zaku iya bibiyar mu a
FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
TELEGRAM⇨
https://t.me/Miftahulilm2
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248