DUNIYAR MATA

DUNIYAR MATA.


Mata suna É—abi'u mabanbanta, yana daga cikin É—abi'un su, daraja soyayya, hira/tattaunawa/sadarwa, kyau/Æ™awa/ado da kuma dangantaka musamman ta Æ™awance. Suna É“ata lokaci mai yawa wurin nuna goyon baya, taimakawa da kuma kulawa da juna. Hankalin su ana auna shi da yadda suke jin (feeling) da kuma karfin dangantakar su. Sukan ji su a cike ta hanyar rabawa da kuma alaÆ™antuwa. 

Kowani abu a duniyar Mata, yana bayyana waɗan nan abubuwa ne. Maimakon gida Birane da dogayen Gidaje, mata sun fi buƙatar gina alaƙa, ta hanyar kasancewa tare da juna cikin girmamawa, soyayya da haɗin kai. Dangantaka tana da matuƙar muhimmanci gare su fiye da aiki da kuma kimiyya da fasaha. A hanyoyi daban-daban, Duniyar Mata tana kishiyantar Duniyar Maza.

Su, ba su sanya unifom (don nuna iko ko kwarewa). Suna jin daɗin sanya sutura mabambanta a rana ɗaya, ya danganta da yanayin da suke ciki. Maganar sirri, ko tsegumi, musamman akan yanayin shigar su, yana da matuƙar tasiri, za su sauya Ƙaya mai yawa daga zaran yanayin su ya sauya.

Hira yana da matuƙar daraja a Duniyar Mata. Su labarta sirrin su ya fi cimma muradi da samun ci gaba muhimmanci. Magana da alaƙantuwa, wasu maɓuɓɓugar annashuwa ne a gare su.
Wannan yana yiwa Maza wahalar fahimta. Maza suna da fahimtar labartawa da saurin alaƙantuwar da Mata suke yi, kamar yadda suke ji ne a yayin da suka yi nasarar gasa, suka cimma muradi ko suka magance wata matsala.

Maimakon zama kwararrun masu cimma buri, su Mata kwararru ne wurin kulla alaƙa. Sun fi damuwa da nuna kirki, ado, soyayya, da kulawar su. Maza biyu za su tafi cin abincin rana don tattaunawa kan ayyukan su ko kasuwancin su; suna dai da matsalar magancewa. Bugu-da-ƙari, su Maza suna tafiya gidan cin abinci ne don su samu isasshiya kuma mafi saukin hanyar cin abinci: babu cefane, babu zaman jiran dafuwa, babu wanke-wanke. Amma a wurin Mata, tafiya gidan cin abinci, dama ne na nunawa kulawa wa dangantaka, za su bayar da goyon baya kuma za su karɓa daga kawayen su. Mata, maganar su a gidan cin abinci a fili take, kamar dai tattaunawar da ke tsakanin Likita da Majinyaci.

A Duniyar Mata, kowace mace ta karanci Psychology, kuma kowace tana da digiri na biyu (Msc) a fannin bayar da shawara. Suna sanya kan su cikin ci gaban da ba na su ba, a ruhance, da dukkan abinda zai nuna kulawa ga rayuwa, ko ya kawo waraka da haɓaka. Duniyar Mata a kewaye take da Shaƙatawa, Lambuna, Ƙantuna, da kuma Gidajen cin abinci.

Mata suna da ilhama, sun samu wannan ilhama ne tun tsawon shekarun da suka ɗauka suna yin kane-kane cikin muradun wasu. Sukan yi alfaharin kasantuwar su muradi kuma shaukin wasu. Alamun soyayya mai ƙarfi a duniyar su, shi ne, kai ɗauki da taimako ga wata mace ko da ba ta nemi taimakon ba.

Tabbatar da kwarewar wani, bai da muhimmanci a Duniyar Mata, bayar da agaji ba laifi ba ne, kuma neman agaji ba ya nuna rauni. Ga Namiji, zai ji tamkar an tozarta shi, saboda idan Mace ta ba shi shawara, ba ya jin ta yaye masa hazon da ya lulluɓe damar zai iya yin aikin da kan shi. Mace ba ta da Masaniyar Namiji na yin wannan tunanin tozarcin, saboda a duniyar ta, kamar karin Gashi ne cikin Sheƙar ta; ka mata agaji. Hakan zai sa ta ji ana son ta, ana nuna kulawa gare ta. Amma kawo agaji ga Namiji (idan ba shi ya buƙata ba) zai sa ya ji, an tauye kwarewar sa, an tallata raunin sa, kuma ya ji tamkar ba a son sa.

A Duniyar Mata, alamu ne na nuna kulawa, bayar da shawara da nuna zaɓi. Mata sun yarda da cewa, duk abinda yake kan aiki, to zai yi aiki fiye da yadda yake yi. Daga cikin tsarin halittar su, akwai son inganta abubuwa. Idan suna kulawa da wani, kai tsaye suke nuna abinda zai ingantu kuma su nuna yadda za a yi. Bayar da shawara da kuma bayyana ƙakkarfan ƙushe, alamu ne da soyayya a duniyar Mata.

Duniyar Maza tana da bambanci. Maza kwararrun masu kawo maslaha ne. Idan abu yana aiki, tambarin su, shi ne; "Kar ka sauya shi", shawarar su, shi ne, a bar shi tunda yana aiki. "kar ka daidaita shi, har sai in karyewa yayi". Wannan gama-garin furuci ne a Duniyar Maza.

Idan Mace ta so ta gyara Namiji, sai ya ji tamkar tana son ta daidaita shi ne. Yana karɓar sakon cewa, a karkace yake. Ita ba ta san cewa, kokarin agaza maza (ba tare da sahalewar sa ba) zai ji kamar kokarin tozarta shi take son yi ba. Ita a tunanin ta, tana taimaka masa don ya haɓaka ne.

Yacin na gaji. Zan fita a DUNIYAR MATA, nan kusa zan shiga DUNIYAR MAZA.

 ku biyo ni.

© Prof. Sufyan
Post a Comment (0)