DUNIYAR MAZA

DUNIYAR MAZA.


Maza suna daraja iko, kwarewa, wadata, da kuma nasara. Kodayaushe suna yin abubuwa ne domin nuna kan su, su haɓakar da ikon su, da kuma kwarewar su. Ana auna hankalin su ne ta hanyar damar da suke da shi wurin cimma sakamako. Samun nasara da kammala wani aiki suna sanya su jin sun wadatu.

Kowani abu a duniyar Maza, yana bayyana waɗan nan abubuwa ne. Hatta suturar su an tsara shi don nuna kwarewa da ikon su ne. Ƴan sanda, Sojoji, Injiniyoyi, Ƴan kasuwa, Matuƙa, Maƙaniƙai, da Sarakuna, dukkan su suna sanya Unifom ko akalla Hular kwano don bayyana iko/matsayi da kwarewar su.

Ba su zama kamar waɗanda suke da digiri a Psychology ba, ba su da lokacin karantar kan su, ballantana sauran Mutane. Sun fi bayar da tunanin su ga abinda ke faruwa a wajen Ƙofa, kamar farauta, Su, da tseren mota. Suna da sha'awar labarai, yanayi, da kuma wasanni. Ba su cika damuwa da karanta labarin soyayya ko labarin taimakon kai ba. Sun fi buƙatar abubuwa fiye da Mutane da kuma shauki. Har yau a wannan Duniyar, a yayin da Mata suke kambama soyayya, su kuwa Maza sun fi kambama motocin alfarma, na'ura mai ƙwaƙwalwa da abubuwan fasaha masu ƙarfi. Maza sun ƙewaye kan su da abubuwan da zai taimaka musu wurin bayyana iko, ta hanyar ƙirƙirar sakamako da cimma muradi ko ciƙar buri.

Cimma buri yana da matuÆ™ar muhimmanci a cikin Duniyar Maza, domin hanya ce ta nuna kwarewar su, kuma su ji daÉ—in kan su. Kuma don su ji daÉ—in kan su, dole su cimma waÉ—an nan muradai da kan su. Bazai yiwu wani ya cimma musu ba. Maza suna yin alfaharin yin abubuwa da kan su. Cin gashin kai, alamu ne da ke nuni da wadatuwa, iko da kuma kwarewa. 

Fahimtar waɗan nan ɗabi'un Mazan, zai taimakawa Mata fahimtar dalilin da yake sanya Maza daƙewa idan aka gyara su ko aka faɗa musu abinda za su aiƙata. A bawa Namiji shawarar da bai nema ba, kamar an yanke cewa, bai san me zai aikata ba. Ko bazai iya yi da kan shi ba. Hakan na gigita ƙimar maza matuƙa, domin batun nuna kwarewa, yana da matuƙar muhimmanci a Duniyar Maza.

Saboda yana iya sarrafa matsalolin sa da kan sa, Namiji bai cika yin magana akan matsalolin sa ba, har sai in yana buƙatar shawara. Yana kafa dalili da cewa; "Me zai sa in sanya wani dabam, bayan zan iya yi da kai na?". Yana aje matsalar wa kan sa, har sai in yana bukatar taimako daga wani don samun maslaha. Neman taimako, bayan za ka iya yi da kan ka, yana ɗaukar sa a matsayin alamun rauni. Bayan haka, idan har ya tabbata yana buƙatar taimako, to alamu ne na wayewa ya samo shi. A wannan yanayin, sai ya nemi wanda yake girmamawa sannan ya labarta masa matsalolin sa. Yin magana akan matsala a duniyar Maza, kamar tura goron gayyata ne ga shawara kai tsaye. Shi kuma wanda aka labarta masa matsalar, zai ji an karrama shi ne da aka ba shi wannan damar. Kai tsaye yake sanya Hular kwanon gyara, ya ɗan saurara na ɗan ƙanƙanin lokaci, sannan ya fara ƙwaranya gwala-gwalan shawarwari.

Wannan al'adar Mazan ne dalilin da ya sa suke da saurin bayar da shawara daga zaran Mace ta labarta masa matsalar ta. A yayin da Mace ta bayyana dalilin fushin ta, ko ta fito fili ta bayyana matsalar ta na wannan yini. Cikin kuskure Namiji yake tsammanin kyawawan shawarwari take buƙata. Nan da nan yake sanya Hular kwanon gyaran sa, sannan ya fara bayar da shawara; wannan shi ne hanyar nuna soyayya, kuma hanyar ƙoƙarin taimaka mata don ta dawo daidai, ta hanyar magance mata matsalolin ta. Yana son zama mai amfani a gare ta. Yana jin zai samu darajawa daga gare ta, kuma ya zama wanda ya cancanci soyayyar ta a yayin da yayi amfani da damar sa ya magance mata matsalar ta.

Daga zaran ya bayar da mafita, amma duk da haka ba ta huce ba, ba ta kuma yaba ba, yana mishi wahalar sake sauraron ta. Saboda ba ta daraja shawarar sa ba, sai ya ji ba shi da wani muhimmanci a wurin ta. Bai san cewa, ta hanyar sauraro cike da tausayi da kuma nuna damuwa za ta goyi bayan sa ba. Bai san cewa a Duniyar Mata, labarta matsaloli ba goron gayyata ne na bayar da maslaha ba.

Na gaji.... 
Akwai tambaya?

© Prof. Sufyan
Post a Comment (0)