HUKUNCIN MAI KOMAWA ZUNUBI BAYAN YA TUBA

HUKUNCIN MAI KOMAWA ZUNUBI BAYAN YA TUBA 


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaykum warahmatullahi wabarakatuhu. Malam dafatar antashi lafiya, kuma irin taimakon da kake da kar6a fatawowin jama'a, Allah ya saka maka da gidan aljanna, iyalan ka Allah ya qara sanya musu albarka ya kiyaye maka su. 

Malam tambaya ta anan itace, nine nake aikata aiki maras kyau. Nayi tuba nayi tuba, har alqawari nayiwa Allah cewar ba zan sake ba bayan nayi sallah nayi addua, Amma saida na sake aikata wannan abin bama sau 1 kuma bakomai bane illa kallon fina-finan batsa. Tau malam don Allah yanxu menene hukunci na a wurin Allah. Kuma ka taimaka min da shawara da Allah. 
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Aikin Zunubi yana daga cikin abinda Ubangiji yake jarabtar bawansa dashi. Kuma ya buɗe mana hanyar tuba da kuma istighfari domin samar mana da mafita daga Qangin zunubi.

To amma ita tuba bata zama cikakkiya kuma mai amfani ga bawa har sai mai yinta ya cika sharudan nan guda uku :

1- Yin nadama bisa laifukan baya.
2- Rabuwa da aikin sa'bon nan take ba tare da jinkiri ba.
3- Daukar niyyar ba zaka sake aikatawa ba, har abada.

- To idan kuma akwai hakkin wani, wajibi ne ka mayar masa, ko kuma ka nemi yafewarsa.

To duk tuban da ta cika waɗannan sharudan ita ce cikakkiyar tuba. Kuma koda Allah ya jarrabi mutum da komawa cikin zunubin ba za'a kirashi Mayaudari ba. Kuma idan ya sake tuba Allah zai gafarta masa. Koda zai yi haka fiye da sau dubu.

Shine wanda Manzon Allah (saww) yake cewa : "MAI TUBA DAGA ZUNUBI KAMAR WANDA BASHI DA ZUNUBI NE".

Amma ya zamanto lokacin da mutum yake tuba akan harshensa ne, amma acikin zuciyarsa yana jin zai koma cikin zunubin, to wannan shine Mayaudari. Tubansa ba Karbabbiya bace. Kuma Allah yakan yi azaba ga masu yin haka.

*Hanyar da zaka bi domin kange kanka daga wannan shine :*

- Kodai ka rabu da waya mai shiga internet, Ko kuma ka dena shiga Shafukan batsa.

- Ka kori shaidan daga kusanci dakai ta hanyar yawaita Karatun Alqur'ani da zikirin Allah ako yaushe.

- In da hali kaje kayi aure. In babu hali ka yawaita azumi. Idan kuma kana da auren, to duk abinda ke jikin wadancan shaitanun da kake kallo, to akwaishi jikin Matarka.

- Ka rika yin sallar nafila raka'a biyu ko hudu kana Qara tuba duk lokacin da shaidan ya rinjayeka ka aikata zunubi.

- Babban al'amari shine Kaji tsoron Allah ka rika tuna gamuwarka dashi. Kuma ka, sani yana tare dakai aduk inda kake.

Allah ya shiryeka tare damu da zuriyarmu baki ɗaya. Ya kiyayemu daga Sharrin Shaitanun fili da boye da kuma sharrin Miyagun laifukanmu.

WALLAHU A'ALAM.

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Aji Tsoron ALLAH kada achanja mana komai! In anga kuskure asanar damu !
Post a Comment (0)