MACEN DA BA A IYA SAKI 16

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(16)*

 *IDAN YA KIRA KI SHIN FIDARSA KI AMSA*

    Ya "yar uwa mai daraja a duk lokacin da mijinki ya kira ki zuwa shimfidarsa ki amsa masa, kada ki kuskura ki ban zatar da buqatar sa, ina mai horarki kada ki bari ya kwana yana mai fushi dake. 
   Farin jakada babba dan Abdullah Muhammadurrasulullahi saw yana cewa "Idan mutum ya kira matarsa zuwa shimfidarsa taki zuwa, ya kwana yana mai fushi da ita mala'iku za suyi ta tsine mata har sai ta wayi gari". 
   Ya qara da cewa "Idan mutum ya kira matarsa zuwa ga buqatar sa ta amsa masa koda tana kan tanderun waina ne". 
    Wata mahaifiya tana yiwa "yarta nasiha tace " Yake "yata duk lokacin da mijinki ya kira ki zuwa ga shimfidarsa ki amsa masa domin cikin amsa masa zaki samu wasu fa'idoji guda uku daga gare sa, na farko babu wata mata da idonsa zai dunga kaiwa zuwa gareta bayan ke, na biyu zai dunga sauri wajan biya miki dukkanin wasu buqatunki, na uku mala'ikun ubangijin al'arshi zasu yarda dake ". 
   Matan magaba ta sun kasance duk lokacin da sukai sallar isha'i sai mace ta cewa mijinta kana da buqata ta? Idan yana da ita sai ta biya masa, idan kuwa babu sai tayi Alwala ta fara qiyamullaili. 
      Ya "yar uwata mai daraja kiyi kokari wajan biya wa mijinki buqatar sa domin ki rabauta a duniya da lahira, muddun kika kasance mace mai sauri da gaggawa wajan amsa gaiyatar mijinki zuwa shimfidarsa kece macen da nake wa laqabi da macen da ba'a iya saki.
    
*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 17*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)