MACEN DA BA A IYA SAKI 17

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(17)*
 
       *TSORAN UBANGIJI*

  Ya "yar uwata mai daraja ki haskaka tsakanin ki da mahaliccin ki da kuma mijinki da tsoran Allah, da gaskiya da amana ki dauki kyakykyawan darasi daga wajan "yar gidan mai siyar da nono. 
    Wata rana sayyadina umar ya futo kamar dai yadda ya saba da daddare domin ya duba halin da jama'arsa suke ciki, yana cikin tafiya akan hanyar madina sai gajiya ta cimmasa, sai ya kishin gida ajikin wata ka tanga sai yaji wata mata tana cewa "yarta tashi kije wajan nonon can ki cakuda sa da ruwa, sai "yar ta ta tace da ita ya ke umma baki san yau umarnin da sarkin mummunai umar yai ba? Sai tace mai ya yi? Sai tace ya sa anyi kira cikin mutane cewa kada wanda ya sake cakuda nono da ruwa, sai matar nan tace da "yarta tashi kije ki cakuda sa, domin kina wajan da umar baya ganin ki haka zalika dan aiken sa, sai tace ya ke umma idan umar baya ganin mu to ubangijin umar yana ganin mu, bazai yuwuwu muyi masa biyayya agabansa ba amma kuma mu saba masa a bayan sa, take wannan yarinyar ta burge umar yaje ya ne mawa dan sa Asim auranta. 
   Ya ke "yar uwa mai daraja ki dauki kyakykyawan misali daga wannan baiwar wajan gaskiya da tsoran Allah, ki dunga cewa ako da yaushe idan mijina baya ganina to ubangijin mijina yana gani na, tabbas idan kika lazimci wannan siffar ta tsoran Allah haqiqa ubangijin ki zai shiga cikin lamuranki ako da yaushe hatta maganar saki sai dai kijita a wani gidan amma dai ba gidanki ba domin kece macen da nake wa laqabi da macen da ba'a iya saka.

*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 18*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏

Post a Comment (0)