MIJI NA GARI !!!

MIJI NA GARI !!! 


Namiji na gari mutum ne mai tsoron ALLAH da kokarin riko da Sunnah Manzon ALLAH (saw).

Son ALLAH da kuma manzon sa (saw) su suka fi soyuwa gare shi fiye da son kowa har iyayen sa da yan'uwan sa.

Miji na Gari yana kiyaye sallah har da nafilfili, yana kuma tayar da iyalan sa da tarbiyantar da su akan haka, yana halartar wuraren wa'azi gwargwadon iko, kuma yana sanya iyalansa halarta ko ya kaisu, yana azumin farilla da kuma sunnah, sa'annan yana zakkhah idan dukiyar sa ta kai in ba ta kai ba yana kokarin sadaka gwargwadon ikon sa.

Miji na gari mai neman halal ne, cikin kasuwancin sa ba zamba cin amana da sauran su in ko ma'aikacin gomnati ne ba ya cin amanar aikin sa da mutane ko cin hanci kuma yana kiyaye lokaci.

Miji na Gari jajirtacce ne wajen kulawa da iyalansa ta fuskar addinin su, mutuncin su, tarbiyya, ciyar da su da tufatarwa gwargwadon ikonsa da kuma nuna musu kauna.

Miji na Gari ba ya tir da iyalansa, ko mummunar addu'a gare su, yana nasiha da kuma addu'a da jumriya akan hakuri da su, lokaci lokaci kuwa yana zaunar dasu domin nuna musu rayuwa darussan ta da kuma nuna musu kulawa.


Miji na gari ba ya zina, ba ya shirka, ba ya shaye shaye, ba ya sata kuma ba ya karya, gulma, munanawa makwafci, rashin sallah, zama a majalisar munafinci da kuma kalle kalle, ba ya dukan matar sa bare zagi, ba ya kuma gori, yana kuma nuna mata ita mai daraja ce.

_______________________________
👉🏽Yaku 'yan'uwa masu albarka ku kasance da Da'awa Fisabilillah domin ilimintarwa, fadakarwa tare da tunatarwa.
 
👉🏽Biyomu Facebook
https://www.facebook.com/DaawaFisabilillah/

👉🏽Biyomu Telegram
https://t.me/DAAWAFISABILILLAH

👉🏽Biyomu Youtube
https://youtube.com/channel/UCQezh3JEjj6gfvCv6GLZIDA

Dan uwanku a musulunci
      ABU--MUS'AB ✍️
      ABU--UNAISA ✍️
Post a Comment (0)