ZINA BA TA DAUKAN HUKUNCIN AURE
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum malam ina da tambaya, Yaro ne karami wanda bai balaga ba, sai wata matar aure ta ringa kiransa tana zina dashi. To sai bayan wasu shekaru masu yawa matar ta daina zina dashi sai matar ta haifi yarinya mace sai shi wannan yaron yaga wannan 'Yar matar kuma yana son ya auri yarinyar, shin ya halatta ya aure ta ?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikum assalam, Tun da alkalami bai hau kansa ba, ai abin da ya yi ba sunansa zina ba shi a bangarensa, sannan zina ba ta daukar hukunce-hukuncen aure a yawancin wurare.
Ya halatta ya aure ta, tun da ba da maniyinsa aka halicce ta ba, tare da cewa barin auran shi ne ya fi a fahimtata, tun da babu tabbacin yarinyar da zai aura din 'yar halal ce, tun da babarta mazinaciya ce, kin ga idan BALLI ya tashi daga baya ran ma'auratan zai iya tashi.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ