TAIMAKON MABUKACI YA FI KA KOMA AIKIN HAJJI BAYAN ZUWANKA NA FARKO!

TAIMAKON MABUKACI YA FI KA KOMA AIKIN HAJJI BAYAN ZUWANKA NA FARKO!


.
Mutum ya bayar da dukiyarsa ga wanda bashi ya tauye masa don ya biya bashin, ko ya bayar da ita ga Matalauci, ko wanda iyalai suka yi masa nauyi don ya kula da iyalinsa, ko ya ba mai rainon maraya don ya yaye masa wahala, ya fi alkhairi fiye da mutum ya tafi aikin Hajji sau dari bayan zuwansa na farko.

Domin hakika cusa farin ciki cikin Zuciyar musulmi da taimakon wanda ke cikin kunci da yaye wahalar Mabukaci da taimakon mara karfi ya fi Hajji dubu bayan na farilla.

Allah Ya bamu ikon taimakawa mabukata.

*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*ANSAR.*
*22nd Jun, 2018.*
.
*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*
Post a Comment (0)