WACE CE UMMU SHARIK RADHIYALLAHU ANHA..

WACE CE UMMU SHARIK RADHIYALLAHU ANHA..


Sunan ta Gaziyya bint Jaabir bin Hakim Addausiyyah,
Mafi yawan malaman tarihi sunce itace wadda ta kyautar da kan ta ga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, amma bai karɓe ta ba, bata yi aure ba har ta mutu

An karɓo daga Ibn Abbas RADHIYALLAHU ANHU yace, muslunci ya faɗa cikin zuciyar UMMU SHARIK, sai ta muslunta a Makkah, ta kasance ƙarƙashin Abul Askaral dausiy, sai ta kasance tana shiga gurin matan ƙuraishawa a ɓoye, tana kiran su tana kwaɗaitar dasu muslunci, har al'amarin ya bayyana ga mutanen Makkah, sai suka kamo ta suka ce da badan mutanen ki ba da mun aikata miki, dai cewa zamu mai dake zuwa garea su 

Tace sai suka ɗora Ni akan raƙumi babu komai a ƙarƙashin na (babu abun zama) sannan suka bar Ni kwana uku babu abinci babu abin sha , sun kasance idan sun sauka a masauki sai su ɗaure Ni a rana, su kuma su shiga inuwa, sun tsare Ni daga abin ci da abin sha, 
Ana haka watarana sun sauka a inuwa sun daure Ni a rana, sai naji sanyi a ƙirji na da na duba sai naga guga na ruwa, sai nasha kaɗan sai aka cire sai aka sake dawo da shi na sha kaɗan aka cire aka aikata hakan sau da dama, sannan aka bar min har na ƙoshi, sannan aka kwara min sauran ruwan a jiki na da tufafi na
Lokacin da suka farka sai suka ga gurbin ruwa a tare dani kuma suka ganni da kyakkyawar hai'a sai suka ce dani, kin kunce kin ɗaukar mana ruwan mu ki ka sha 
Tace a'a wallahi sai dai a cewa hakan daga al'amari kaza da kaza ya faru 
Suka ce
Idan kin kasance mai gaskiya to lallai addini ki ne mafi alkhairi daga addinin mu, yayin da suka duba abin ruwan su, suka same shi kamar yadda suka barshi, sai suka muslunta a wannan lokacin

📚صفة الصفوة 
*⁦✍️⁩Hauwa T Musa.*
27/11/2021.

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*
Post a Comment (0)