*💫Tambayoyi Da Amsa A Kan Hukunce-Hukuncen Azumi.*
*✨سؤال وجوب في أحكام الصيام.*
Wallafar:
*Sheikh Muhammad bn Salih Al-Uthaimin.*
.
.
(5) YIN JIMA'I A WATAN RAMADAN.
Tambaya: Mutum ne ya yi kwanciyar aure da matarsa a cikin watan Ramadan ba tare da ya fitar da maniyyi ba, tare da fahimtar cewa kaffara na wajaba ne idan an fitar da maniyyi, wato ya san cewa idan aka yi jima'i aka fitar da maniyyi za a yi kaffara amma be san hakan a kan jima'i da ba a fitar da maniyyi ba.
Amsa: Idan ya yi imani da hakan, babu komai a kan shi, ba zai rama azumin ba, saboda faɗin Allah:
{...رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذۡنَاۤ إِن نَّسِینَاۤ أَوۡ أَخۡطَأۡنَاۚ.. }
Ma'ana: *"Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure."*[Surah Al-Baqarah: 286]
Mu haɗu a tambaya ta gaba.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*▫️Ansar.*
*📚Irshadul Ummah.*
Ku kasance da mu a Whatsapp ta wannan number *08166650256.*
Telegram:
https://t.me/irshadulummah1