ZA MU IYA TAYA KRISTA MURNAR BIKIN HAIHUWAR ANNABI ISA ?

ZA MU IYA TAYA KRISTA MURNAR BIKIN HAIHUWAR ANNABI ISA ?


Tambaya:
Assalamu alaikum
Malam muna da makota Krista, ko za mu iya taya su murnar zagayowar Kirsimeti ?

Amsa
Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda suna yin hakan ne don girmama d'an Allah, mu kuwa Musulmai Annabi Isa bawan Allah ne da kuma Rai cikin rayukan da Allah ya halitta a wajanmu, kamar yadda Allah ya Yi bayani a cikin suratun Nisa'i da Ma'idah.
Allah Madaukaki Bai haifa ba, ba a Kuma haife Shi ba, Shi kadai yake ba Shi da abokin tarayya.
Taya su murna yana nuna yarda da abin da suke riyawa, Kudurce cewa Annabi Isa d'an Allah ne kafirci ne Kuma ya sabawa abin da suratul Iklasi ta kunsa.

Su kan su kristoci sun Yi sab'ani mai yawa game da ranar da aka haifi Annabi Isa, wannan yake nuna rashin tabbacin haihuwarsa ranar 25/12.

Allah ne Mafi sani

Dr. Jamilu Yusuf ZAREWA
25/12/2021

ZaKu iya Bibiyar Mu a 

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)