DA GASKENE SHUWAGABANNIN SAUDI BA SUSO AYI HAWAN ARAFA RANAR JUMU'A?

DA GASKENE SHUWAGABANNIN SAUDI BA SUSO AYI HAWAN ARAFA RANAR JUMU'A?


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu Alaikum Malam.  Wai da gaskene shuwagabannin Saudi ba suso ayi hawan Arafa ranar Jumua? Wai saboda tarihi ya nuna a lokacin za6a Karbe milki a hannunsu?
:
*AMSA*👇
:
Wa alaikumus salamu warahmatullah.

Wannan maganar karyace tareda izgili ga addini, Allah yakare mana imaninmu.

1. Annabi ﷺ yayi arfa ne ahjjatul wada'i shekara ta tara bayan hijira hajjin karshe arayuwarsa.

Ansamo daga Umar Dan Khaddab Allah kara masa yarda, lallai wani mutun daga cikin yahudawa yace: ya Amirul Muminina, akwai wata aya acikin littafinku da ace cikinmu ne jama'ar yahudawa ta sauka da munriki wannan yinin idi duk shekara inta zagayo, sai yace: wace aya ce? Sai yace: (ALYAUMA AKMALTU LAKUM DINAKUM, WA ATMAMTU ALAIKUM NI IMATIY WARADITU LAKUMUL ISLAMA DINA). Umar yace: Hakika munsan wannan yinin, da wurinda tasauka ga Annabi ﷺ yana tsaye ne afilin arfa ranar jumu'ah. Imamul Buhari yaruwaitoshi acikin kitabul Imani na Sahihul Bukhariy, babin karuwar imani da tawayarsa, babina na: 33. Hadisi na: 45.

Darasin da zamu dauka awannan hadisin yana da yawa kadan daga ciki:

A. Annabi ﷺ yayi arfar Hajjatul wada'i ranar Jumu'ah ne, saboda haka babu wani tarihi da ya nuna za'a kwace mulki daga hannunsu amusulunce.

B. duk abinda yacika zai taragewa ne ahankali, harda Imani.

C. Yahudawa sunsan gaskiyar musulunci hassada kawai ke hanasu bi.

D. Yahudawa larabawan bidi'a ne.

E. Sahabbai basu bidi'ah.

F. Ba arena bidi'a komai karancinta.

G. Wamnan ayar bayanta ba wani hukunci da aka sake saukarwa bayanta na ibada, sai dai na tauhidi da akida, ayar da aka saukar karshe gabaki daya akur'ani ayar dake bakara: 281.

H. Ba'ayarda ayi wani biki ko idi ko hutun shekara Ashekara ace duk in shekara ta kewayo ayi sai biyu kawai, Idin layya dana azumi. Lokacin da Annabi ﷺ yazo madina yasamesu suna wasa duk shekara aranaku biyu sai yace: (HAKIKA ALLAH YA CANZA MUKU SU DA WASU YINI BIYU DA SUKA FISU ALHERI, YININ SALLAR LAYYA DA TA AZUMI ).

Abu dawud:1134.

Saboda haka babu:
X'mas day, Maulidi day, da children day, da Birth day, da independence day, Democracy day,  da workers day, da Teacher day, da Hijab day, day, day, day,... duk babu su amusulunci.

I. Ashekarar 2006. Dani akayi arfa, kuma aranar Juma'ah akayita, kuma ba'asamu hajjinda yatara dan mutun kafinsa irinsa ba,  kuma ba wanda aka kwacewa mulki kuma ba wanda yamutu cikin sarakunan, balle ma wannan shekarar akafi saukin mutuwa a aikin hajji.

J. Idan Arfa ta kama ranar Jumu'ah, to duk kasashen larabawa dake kewayen makkah, zakaga sunyi cincirindo sunzo aikin hajji hadda shuwaganni.

K. Sai dai hadisin da yace: wai arfa ranar  Jumu'ah dai dai take da Arfa arba'in 40, bai ingantaba.

Allah yabamu ikon fahimtar addininmu.

Wallahu ta ala a alam.

Shafi'u Shehu Minna.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)