DAGA CIKIN KURA-KUREN MAI SALLAH

DAGA CIKIN KURA-KUREN MAI SALLAH


 DARASI NA FARKO-(1)

 KUSKURE NA DAYA
1-Wasu daga ciki n masu yin sallah suna yin karatun sallah a zuci ba tare da motsa Harshen su ba,kuma suna yin hakan wajen Azk na Ruku’u da Sujada.

ABINDA YAKE DAIDAI
{A lokacin karanta Fatiha da Sura ac ikin sallah waji bi ne mutum ya motsa harshen sa dan mai yin sallah ya jiyar da kansa abin da yake karantawa,sannan haka zai aikata lokacin da yake Azkr da addu’a acikin ruku’u da sujada da zaman Tahiya da makamantan su}

KUSKURE NA BIYU
2-Wasu daga cikin masu bin Liman lokacin da suka shiga masallaci Liman yana RUKU’U KO SUJADA,sai su yi KABBARA daya kadai su shiga cikin ruku’u ko sujada

ABIN DA YAKE DAIDAI
Idan mutum ya shiga masallaci a lokacin da Liman yake cikin RUKU’U ko SUJADA zai bi liman ne da yin KABBARORI guda biyu kabbara ta farko tare da Niyyar itace kabbarar Harama,ta biyu kuma ta shiga ruku’u ko sujada, amma idan babu wadatar lokacin da zai yi hakan,to sai yayi kabbara guda daya wato kabbarar harama sai ya shiga ruku’u ko sujada.

KUSKURE NA UKU
Rashin bayyana fadar AMEEN bayan gama Suratul Fatiha ga Mamu da Liman

ABIN DA YAKE DAIDAI
Shine Liman da Mamu zasu bayyana fadar AMEEN bayan gama FATIHA acikin sallar da ake bayyana karatu.
@ﺳﻤﺎﺣﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﻋﺒﺪﺍﻟﻌﺰﻳﺰ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﺑﺎﺯ ‏] ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
‏@ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﺻﺎﻟﺢ ﺍﻟﻌﺜﻴﻤﻴﻦ ‏] ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
‏@ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺠﺒﺮﻳﻦ ‏] ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
‏@ﻓﻀﻴﻠﺔ ﺍﻟﺸﻴﺦ / ﺻﺎﻟﺢ ﺑﻦ ﻓﻮﺯﺍﻥ ﺍﻟﻔﻮﺯﺍﻥ ‏] ﺣﻔﻈﻪ ﺍﻟﻠﻪ
@ﻭﺍﻟﻠﺠﻨﺔ ﺍﻟﺪﺍﺋﻤﺔ ﻟﻺﻓﺘﺎﺀ
ﺟﺰﺍﻫﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺧﻴﺮ ﺍﻟﺠﺰﺍ

Allah ne mafi sani

Allah ya bamu ikon gyarawa,mu haɗu a Darasi na gaba insha Allah
Post a Comment (0)