IDAN MUTUM NA CIKIN MATSANANCIYAR DAMUWA MENE YA KAMATA YAYI
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamou aleikoum, idan mutun na cikin matsananciyar damuwa mi ya kamata ya yi dan magance ta? dan Allah kumin kokari na samun amsa da wouri.
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus salam, Ibn Mas'ud Allah ya qara masa yarda ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Wata damuwa ko baqin ciki ba sa taɓa samun mutumin da ya karanta wannan addu'ar, face Allah ya tafiyar masa da wannan damuwa da baqin ciki, kuma ya canja masa da kwaranyewar damuwar:
"اللَّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ وَابْنُ عَبْدِكَ وَابْنُ أَمَتِكَ ، نَاصِيَتِي بِيَدِكَ ، مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ ، عَدْلٌ فِيَّ قَضَاؤُكَ ، أَسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ ، سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ ، أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَدًا مِنْ خَلْقِكَ ، أَوْ أَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ ، أَوْ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ : أَنْ تَجْعَلَ الْقُرْآنَ رَبِيعَ قَلْبِي ، وَنُورَ صَدْرِي ، وَجِلَاءَ حُزْنِي ، وَذَهَابَ هَمِّي ؛ إِلَّا أَذْهَبَ اللَّهُ هَمَّهُ وَحُزْنَهُ ، وَأَبْدَلَهُ مَكَانَهُ فَرَجًا".
*MA'ANA:*
"Ya Allah ni bawanka ne, ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka, makwarkwaɗata (mafuskantata) a hannunka take, hukuncinka zartacce ne a kaina, kuma qaddararka a gare ni mai adalci ne, ina roqonka da dukkan sunayenka, wanda ka ambaci kanka da shi, ko ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka sanar da shi ga wani daga cikin halittarka, ko ka keɓance kanka da saninsa a cikin ilimin fake (gaibu) da ke wurinka, ka sanya Alqur'ani ya zama daɗi ga zuciyata, ya zama haske ga qirjina, ya zama kwaranyewa ga baqin cikina, ya zama mai tafiyar da damuwata".
A qarshen hadisin an ruwaito cewa Sahabbai sun tambayi Manzon Allah ﷺ cewa; shin ba ma sanar da wannan addu'ar ba? Sai ya ce: "Tabbas, ya kamata wanda ya ji addu'ar nan ya sanar da ita""
A Duba Musnadu Ahmad hadisi mai lamba ta 3712. Ko a duba Sahihu Ibn Hibban hadisi mai lamba ta 972.
Wanda ba zai iya yi da Larabci ba ya yi da Hausa.
*FA'IDOJIN WANNAN HADISI*:
1. Idan damuwa da baqin ciki suka dami mutum to ya lizimci wannan addu'ar.
2. Yawan karanta Alqur'ani yana taimakawa wajen yaye baqin ciki da damuwa.
3. Allah kaɗai ne yake iya yaye wa mutum baqin ciki da damuwa ba waninsa ba.
4. Duk idan baqin ciki da damuwa suka matsa wa mutum ya yi addu'a ne, ba zuwa gidan boka ko ɗan tsubbu ba, musamman ma wannan addu'ar.
5. Idan mutum ya sami labarin wannan addu'ar shi ma ya yi qoqarin sanar da waninsa.
6. Sahabbai ba sa rowar sanar da al'umma ilimoman da suka koya a wurin Manzon Allah ﷺ. Da sauran fa'idoji da dama.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ