Ramadaniyyat: 1443 [1]
Masu Tauye Mudu (1)
1. Allah (S.W.T) yana cewa:
(Tsananin azaba ya tabbata ga masu tauye ma'auni. Waɗanda idan suka auna daga wajen mutane suna cikawa fal. Idan kuwa su za su aunar da mudu ko sikeli, to sai su tauye. Yanzu waɗannan ba sa zaton cewa su lalle za a tashe su? A ranar mai girma? Ranar da mutane za su tsaya gaban Ubangijin talikai?" [Suratul Muɗaffifina aya ta 1-6].
2. Da waɗannan ayoyi Allah (S.W.T) ya buɗe Suratul Muɗaffifina, watau masu tauye mudu. Allah (S.W.T) ya buɗe Surar da kakkausan alkawarin narko da tsananin azaba da ya tadanar wa musu wannan mummunan aiki, tare da faɗar laifin da suka aikata.
3. Ubangiji (S.W.T) ya bayyana irin yadda wadannan mutane suke mu’amala da 'yan'ywansu, watau a yayin da suke harkar kasuwanci da su, wajen saye da sayarwa; inda za su yi awo sai su cika ma'auni fal cikakke ba sa rage komai. Amma idan su suka zo aunarwa, to a nan kuma za su yi ƙwange, su rage wa mutane haƙƙoƙinsu ta wajen awo da mudu ko sikeli.
Rana Mai Girma:
4. Allah (S.W.T) ya nuna mamakin sha’anin waɗannan mutane tare da cewa suna nuna sun yi imani da Allah (S.W.T) da ranar lahira, amma kuma duk da haka suke yin wannan mummunan aiki. Shin ba sa zaton cewa, akwai ranar da za a tashe su daga ƙaburburansu, a sake dawo musu da rayukansu a tsaida su gaban Allah (S.W.T) a cikin wata rana mai girman sha’ani? Ranar da hatta annabawa kowa cewa yake yi "Nafsi-Nafsi", wato (takaina nake, takaina nake) [Duba, Bukhari#3340,#4712 da Muslim#194, #195].
5. Shin waɗannan mutanen ba sa tsammani akwai wannan ranar tana tafe? Ranar da Allah ya siffatanta da cewa:
Ma’ana: "(kuma (duk) muryoyi su yi ƙasa-ƙasa saboda (girman Allah) Mai rahama, sannan ba za ka ji (komai) ba sai raɗa) [Suratu ƊaHa aya ta 108].
6. Ranar da babu wanda da zai ceci mutum daga Allah (S.W.T) sai aikinsa na ƙwarai. Ranar da dukiya da ‘ya’ya da dangantaka ba za su yi amfani ba:
(A ranar da mutum yake guje wa ɗan'uwansa. Da uwarsa da ubansa. Da matarsa da 'ya'yansa. Kowane mutum daga cikinsu a wannan rana yana da lamarin ya sha kansa) [Suratu Anas aya ta 34-36].
7. Don haka rana ce da kowa yake ta kansa:
(Ranar da dukiya da ‘ya’ya ba sa amfani. Sai dai wanda ya zo wa Allah da lafiyayyar zuciya) (Suratu Shu'ara aya ta 88-89)
Lafiyayyar zuciya ita ce: zuciyar da babu shirka a cikinta babu riya, babu hassada, ba qulli ga wani, babu mugun nufi da sauran cututtukan zukata.
8. Mutanen da suke zaluntar jama'a ba sa tunanin akwai ranar zuwan wannan rana. Da a ce suna zato cewa akwai ta, to da ba su rika zalutntar wasu ba, ballanta a ce suna da yaqini da zuwanta. Lalle a akwa abin mamaki tattare da irin waɗannan mutane.
A nan Allah yana nun mana cewa, duk mutumin da ya yarda kwai lahira da kuma hisabi, kuma ya yi imani cewa, akwai wuta da aljanna, to bai dace an samu irin wannan a tare da shi ba. Watau ba zai yiwu a same shi da tauye haƙƙin jama’a ba.
Waɗannan ayoyoyi gargaɗi ne mai tsanani ƙwarai ga mutanen da suke cutar da jama’a. Idan suna mu’amala da mutane, ba sa yarda a cuce su ba, watau akwai su da bin ƙwaƙƙwafi da ƙeƙe-da-ƙeƙe a kan haqqinsu, har sai sun karve shi cikakke. To amma a yayin da a ka zo karva daga wajensu, to a lokacin ne za su yi ta bin hanyoyi da dabaru don su tauye wa mai karba haƙƙinsa.
Telegram
https://t.me/Miftahulilm2