Assalamu alaikum,
Ina rokon Allah ya karɓa mana dukkan ibadunmu, ya sa mun dace.
Ya kamata mu sani cewa Ƙarewa ko wucewar watan Ramadan ba ya nuna cewa ibada ta ƙare, a'a, ana so ka cigaba tare da dawwama akan bauta ga Allah tsawon rayuwarka tare da ɗabbaka darussan da aka koya a Ramadan kamar su sallar dare, karatun Qur'ani, sadaqa dashi kansa azumin da sauransu.
Allah ya na cewa a ayar ƙarshe ta Suratul Hijr:
"واعبد ربك Øتى يأتيك اليقطين"
Ma'ana ka bautawa Allah har mutuwa ta zo maka.
Malamai na cewa:
"كن ربانيا ولا تكن رمضانيا"
Wato ka zamanto bawan Allah ba wai bawan watan Ramadan ba. Kar ace kawai a Ramadan ne zaka bautawa Allah.
Muna fatan Allah ya karɓa mana dukkan ibadunmu.
عيدكم مبارك، تقبل الله منا ومنكم.